Zargin Almundahanar ₦1.35bn: Kotun Ƙoli Za Ta Warware Taƙaddamar EFCC Da Lamiɗo
[ad_1]
A ranar Juma’a, 16 ga Janairu, 2026, Kotun Koli za ta yanke hukunci kan shari’ar zargin karkatar da Naira biliyan 1.35 da aka dade ana buga shari’a tsakanin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, da ‘ya’yansa maza biyu – Mustapha Lamido da Aminu Lamido.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na sada zumunta a ranar Alhamis, inda ta ce, kotun koli ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar 25 ga Yuli, 2023, wanda ya wanke Lamido daga kan tuhume-tuhumen.
Hukumar EFCC, wacce ba ta gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba, ta shigar da ƙara a ranar 31 ga Yuli, 2023, tana neman soke hukuncin tare da mayar da shari’ar zuwa kotun da aka fara shari’ar don ci gaba da yanke hukunci.
[ad_2]
Source link