Shugabar Tanzania Ta Bai Wa ’Yarta Da Sirikinta Muƙamin Minista
[ad_1]
Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, ta sanar da sabon jerin ministocinta, inda ta ƙirƙiri sabuwar Ma’aikatar Matasa kuma ta ƙara adadin ma’aikatun gwamnati zuwa 27.
A cikin sabbin naɗe-naɗen da ta yi, ta naɗa ’yarta, Wanu Hafidh, a matsayin ƙaramar ministar ilimi, sannan ta naɗa sirikinta, Mohamed Mchegerwa, a matsayin ministan lafiya.
Wannan ya janyo cece-kuce da muhawara mak zafi a tsakanin al’ummar ƙasar.
Shugabar ta sake dawo da wasu tsofaffin ministoci guda bakwai, amma ta cire tsohon mataimakin firaminista, Dotto Biteko, da tsohuwar shugabar majalisa, Tulia Ackson.
Sabbin naɗe-naɗen na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Shugaba Samia ta kafa kwamitin bincike kan zanga-zangar bayan zaɓe, inda jam’iyyun hamayya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam suka zargi jami’an tsaro da kashe mutane da dama.
Duk da haka, hukumomi ba su bayyana adadin waɗanda suka rasu ba.
Shugabar ƙasar ta lashe zaɓen ne da kashi 98 na ƙuri’un da aka kaɗa.
[ad_2]
Source link