Sabuwar Yarjejeniyar FGN-ASUU: Tinubu Ya Amince Da Ƙarin Sabon Alawus Ga Farfesoshi


Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da sabuwar yarjejeniyarta da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), inda Shugaba Bola Tinubu ya amince da ingantattun tsare-tsaren jin dadin malaman, gami da sabon alawus na wata-wata wanda zai sa Farfesoshin Jami’o’i su sami sama da Naira 140,000 a matsayin ƙarin albashi.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana hakan a daren Laraba yayin da yake magana a shirin ‘Politics Today’ a gidan talabijin na Channels, yana mai jaddada cewa, yarjejeniyar za ta ɗore kuma an riga an fara aiwatar da ita.

A cewar Alausa, Shugaban ya amince da yarjejeniyar ne bayan ya tabbatar da cewa akwai isassun kudade, yana mai jaddada cewa Tinubu ba ya yin alkawuran da ba za a iya cikawa ba.

Alausa ya tabbatar da cewa, Gwamnatin Tarayya yanzu tana da albarkatun da za ta iya samar da ƙarin kashi 40 cikin 100 na albashi ga malamai a dukkan manyan makarantu, tare da cika sauran alƙawura guda tara waɗanda aka tsara acikin sabuwar yarjejeniya a fili.

A wani mataki da aka bayyana a matsayin wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, Shugaban ya kuma amince da wani sabon nau’in alawus na Farfesoshi da sauran manya a ɓangaren ilimi.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *