Shugaban IPC: Ci Gaban Wasannin Nakasassu Na Kasar Sin Ya Ba Da Misali Ga Duniya

[ad_1]

Sin ta riga ta zama jagora mai muhimmanci wajen habaka wasannin motsa jiki na nakasassu na duniya da harkokin dake alaka da su, kuma ta ba da misali irin na salonta ga duniya bisa ayyukan inganta hadewar kula da lafiyar jiki da zamantakewa ga nakasassu ta hanyar wasanni.

Shugaban kwamitin gasar wasannin Olympic ta nakasassu wato IPC, Andrew Parsons ya bayyana hakan a jiya Talata. Ya kara da cewa, Sin ta sami sakamako mai ban mamaki a gasar wasannin Olympic ta nakasassu a cikin ’yan shekarun nan, kuma tana kan gaba a cikin masu jerin ’yan wasa a gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta yanayin zafi na dogon lokaci. Bayan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta hunturu ta Beijing ta 2022, Sin ta hanzarta inganta karfinta a kan wasannin hunturu baki daya, kana ta zama wani karfi mai muhimmanci a fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta hunturu. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *