Ƙasashen Afirka 3 na zawarcin kocin Super Eagles Eric Chelle

[ad_1]



Wasu ƙasashen nahiyyar Afirka uku da suka haɗa da Guinea, Angola da Tunisia sun shiga zawarcin kocin tawagar Najeriya ta Super Eagles, Eric Chelle.

Eric Chelle ɗan asalin ƙasar Mali, ya samu ɗaukaka ne bisa bajintar da ya yi wajen jagorantar Najeriya a wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya duk da ba ta samu tikiti ba.

Haka kuma, tauraruwar Eric Chelle ta ci gaba da haska musamman la’akari da ƙwazon da tawagar Najeriya ke yi a gasar Kofin Nahiyyar Afirka da ke gudana a ƙasar Morocco, inda ya lashe wasanni biyar a jere, wanda yanzu haka tawagar ta kai wasan kusa da na ƙarshe.

Kwantiragin Chelle da Super Eagles zai ƙare ne bayan kammala gasar AFCON idan ba a tsawaita yarjejeniyar ba.

Chelle ya shiga cikin jerin masu horarwar huɗu daga Afirka da suka yi bajinta a gasar AFCON ta bana.

Mai masaukin baƙi, Morocco tana da mai horarwa Walid Regragui da Hossan Hasan na Masar da Pepe Thiaw na Senegal da kuma Erik Chelle ɗan Mali mai jan ragamar Super Eagles.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *