Mutum 6 ’yan gida ɗaya sun rasu a Ribas

[ad_1]



Wasu mutum shida ’yan gida ɗaya sun rasa rayukansu sakamakon shaƙar iskar wani sinadari mai guba da ake zargin maganin sauro ne a unguwar Ogale Eleme da ke Jihar Ribas.

Rahotanni sun nuna cewa mamatan sun kwanta barci ne a ɗaki ɗaya a daren Asabar, bayan sun kunna maganin domin kauce wa cizon sauro, sai dai har aka wayi gari ba su farka ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.

Ta ce an gano gawarwakin mutanen ne a safiyar Lahadi, bayan da aka samu ɗakin nasu a kulle, kuma babu wanda ya ga ko ya ji motsinsu tun bayan da suka shiga ɗakin.

“An gano gawarwakin ne a cikin ɗaki bayan da babu wani daga cikinsu da aka gani da safe,” in ji ta.

Wani daga cikin dangin mamatan, mai suna Godwin Ogosu, shi ne ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda.

Ya ce matar ɗan uwansa da ’ya’yansu sun shiga ɗakin tun da dare suka kwanta barci, amma babu wanda ya farka har safiya, kuma ƙofar ɗakin ta kasance a rufe tsawon lokaci.

Ya ce tun da ba a ga fitowar su ba, aka yi tsammanin ko sun fita wani wuri, sai daga baya aka fahimci abin da ya faru.

SP Iringe-Koko ta ƙara da cewa rundunar ’yan sandan ta shawarci al’umma kan ɗaukar wani mataki a hannunsu, face sun sanar da jami’an tsaro.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an kwashe gawarwakin mamatan zuwa asibiti da zummar gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar su.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ribas, Olugbenga A. Adepoju, ya bayyana alhini tare da yi wa iyalan mamatan ta’aziyyar rashin da aka yi.

Ya kuma bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen shida tare da gabatar masa da rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *