Rashin Yarda Da Sauran Abubuwan Da Ke Haifar Da Sabani Tsakanin Nijar Da Benin

[ad_1]

A ranar Litinin ne gwamnatin Jamhuriyar Benin da ke Yammacin Afirka ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai na Jamhuriyar Nijar, a wani abu da masana ke bayyanawa da tabarbarewar alaka tsakanin kasasashen biyu.

A cewar hukumomin kasar ta Benin, sun dauki matakin ne bayan wasu lamura da suka fi karfinsu, kodayake ba ta fitar da wani karin bayani a hukumance kan lamarin ba.

A nata bangare ita ma Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan wannan mataki, in da ta umarci jami’in diflomasiyyar Benin ya saka hannu kan takardar dakatar da aiki, sannan ya bar kasar cikin sa’o’i 48.

Lamarin ya faro ne tun bayan da hukumomin Benin suka dauki matakin korar shugaban hukumar leken asirin Nijar da ke birnin Cotonou da kwamishiniyar ‘yansanda da ke ofishin jakadancin Nijar a Cotonou bisa zargin aikata zagon kasa.

Inda a ranar 1 ga watan Janairu ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta ayyana Seidou Imourana, babban jami’in Diplomasiyyar ofishin jakadancin Benin a matsayin wanda ba a bukatar zamansa a kasar, tare da umartarsa da ficewa daga kasar.

Ba wannan ne karo na farko da kasashen biyu makotan juna ke samun tsamin dangantar Diplomasiyya tsakaninsu ba.

Ko a shekarar 2024 Jamhuriyar Benin ta yi yunkurin dakatar da wani shirin Nijar na shimfida bututun mai zuwa kasashen waje, lamarin da ya sa gwamnatin Nijar ta ce za ta karkatar da aikin domin bi da kasar Chadi.

Kasashen biyu dai na zargin juna da aikata zagon-kasa, makonni bayan yunkurin juyin mulki a Benin da bai yi nasara ba, inda wasu kafafon yada labaran Benin suka zargi Nijar da hannu a kitsa juyin mulkin, kodayake babu tartibiyar hujjar da ta tabbatar da hakan.

Tun bayan juyin mulkin Nijar na watan Yulin 2023, aka rika samun sabani tsakanin kasashen biyu, masu kusanci da juna.

Tun bayan juyin mulkin Nijar na watan Yulin 2023, aka rika samun sabani tsakanin kasashen biyu, masu kusanci da juna.

Me ya janyo takaddamar?

Mutane da dama kan yi mamakin yadda kasashen biyu makusantan juna ke takun-saka tsakaninsu, kasancewarsu al’umma iri daya masu al’adu iri daya, to amma me ya janyo musu wannan takaddama?

Alkasoum Abdourahmane masanin siyasa da al’amuran yau da kullum a yankin Afirka ta Yamma da kasashen Sahel ya ce matsalar ta samo asali ne tun bayan juyin mulkin da aka samu a Jamhuriyar Nijar a 2023.

Masanin diflomasiyyar ya ce matsayar da Benin ta dauka na rashin goyon bayan juyin mulkin Nijar na daga cikin abubuwan da suka assasa matsalar.

‘Bayan juyin mulkin NIjar ta yanke duk wata hulda da kasashen Yamma, to amma ita Benin sai ma ta kara karfafa alakar kawancenta da kasashen musamman Faransa, wani abu da Nijar ke kallo a matsayin barazana gareta”, in ji shi.

Alkasoum Abdourahmane ya kara da cewa yadda Benin ta hada kai da Ecowas wajen yi wa Nijar barazana da yunkurin kai mata hari, shi ma ya taimaka wajen tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu.

Wace illar tabarbarwar alakar ke janyo musu?

Alkassoum Abdourahmane ya ce rashin kyawun alaka tsakanin kasashen biyu na haifar musu mummunar illa, da ya ce tuni ta samu.

Masanin ya ce ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki tabarbarewar alakar na haifar wa kasashen biyu mummunart asara.

”Kusan a iya cewa Jamhuriyar Benin ba ta da wata kasa abokiyar kasuwanci da take amfani da tasoshin jiragen ruwanta kamar Nijar, kuma akwai wasu kasashen Afirka kamar Najeriya da Chadi da ma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda duka ta NIjar kayayyakinsu ke biyowa”.

Ya kara da cewa sakamakon tabarbarewar alakar kasashen biyu an daina sauke wa Nijar kaya a tashar ruwan ta Benin.

”Kuma hakan ya haifar wa kasashen biyu asarar makudan kudaden shiga”, in ji shi.

Haka ma wasu masanan na ganin cewa rashin kyawun alaka tsakanin kasashen biyu na shafar yakin da suke yi da kungiyoyin masu aikata laifuka a cikin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna.

”Kuma wannan na daga cikin manyan illolin da wannan takun saka zai haifar wa kasashen biyu”, a cewar Alkassoum.

Ya kara da cewa akwai iyakokin kasashe uku zuwa hudu a kan iyakar kasashen.

”Akwai iyakar Nijar da Benin da kuma Najeriya, haka ma akwai iyakar Benin da NIjar da kuma Burkina Faso, kuma rashin hadin kan kasashen zai shafi aikin tsaron hadin gwiwa a kan iyakokin”, kamar yadda ya bayyana.

Me ya kamata kasashen biyu su yi?

Abdollay Mustafa masanin harkokin diplosamiiya a jamhuriyar Nijar ya ce abinda ya kamata kasashen biyu su yi shi ne shugabannin su zauna wuri guda domin warware matsalar.

”Ya kamata shugabannin kasshen biyu su zauna su fahimci juna tsakaninsu da Allah, idan ana batun Diplomasiyya sai an kawo batun yarda da juan an kuma kawar da zargi”, in ji shi.

Ahmadou Dankware mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijar ya kuma shaida wa BBC cewa ya kamata shugabannin kasashen biyu su kalli al’umomin da ke wahala a cikin wannan al’amari.

”Yana da kyau shugabannin biyu su fahimci cewa duka al’umominsu na cikin wani kangi na wahala sakamakon wannan matsala, domin warware matsalar, tun da ai ko yaki ma ana yin sulhu”, kamar yadda ya yi karin haske.

Alkassoum Abdurrahman ya ce babu wata hanya da ta fi da lalama wajen warware matsaloli.

”Ya kamata kasashen biyu su zauna su cire mummunan zato da zargi tsakaninsu, domin magance wannan matsalar da ke janyo musu asara ta fuskar tattalin arziki da tsaro”, in ji shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *