AFCON 2025: Za a yi karon-batta tsakanin Najeriya da Aljeriya a kwata fainal
[ad_1]
Najeriya za ta fafata da Aljeriya a wasan kwata fainal na Gasar AFCON ta 2025 da yammacin ranar Asabar a birnin Marrakech, da ke ƙasar Maroko.
Wasan zai haɗa tawagar ƙasashe biyu masu ƙarfi da iya salon taka leda.
Najeriya na da ’yan wasan gaba masu hatsari wajen iya kai hari, yayin da Aljeriya ta kasance ƙasa mafi kyawun masu tsaron baya.
Tawagar ƙasashen biyu su ne kaɗai da suka lashe dukkanin wasanninsu uku a matakin rukuni.
A wasan da ya gabata Najeriya ta lallasa Mozambique da ci 4 da baby a zagayen ’yan 16.
Ɗan wasan gaban Super Eagles Victor Osimhen, tare da Ademola Lookman da Akor Adams ne, sun taimaka wa Najeriya wajen zura ƙwallaye 12 tun farkon fara gasar.
Lookman na daga cikin ’yan wasan da suka fi nuna bajinta a gasar AFCON ta bana.
Sai dai duk da wannan tasiri da suke da shi, Najeriya na fuskantar matsaloli.
A wasan da ya gabata, an hangi Osimhen yana yi wa Lookman faɗa cikin fushi sakamakon hana shi wata ƙwallo.
Hakazalika, ana zargin cewa har yanzu Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), ba ta biya ’yan wasan wasu kuɗaɗen alawus-alawus da suke bi ba.
’Yan wasan sun yi barazana sau biyu na ƙin yin atisaye matuƙar mahukunta ba su ɗauki matakin biyansu haƙƙoƙinsu ba.
Sakamakon saɓanin da aka samu tsakanin Osimhen da Lookman, wasu rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan gaban Galatasaray, ya yi barazanar barin sansanin Super Eagles.
Haka kuma, duk da barazanar da ’yan wasan suka yi na ƙin zuwa birnin Marrakech domin fafatawa da Aljeriya, daga ƙarshe sun isa birnin domin yin wasan.
Kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya ce tawagarsa a shirye ta me, amma ya ƙi yin magana kan matsalolin da ke faruwa da ita.
A ɓangaren Aljeriya kuwa, tawagar na da ƙwarin gwiwa.
Matashin ɗan wasanta Ibrahim Maza ya ce ba sa tsoron Najeriya, domin a cewarsa ƙwallo ɗaya kacal aka zura a ragarsu tun farkon fara gasar.
Aljeriya na da ɗaya daga cikin ƙasashe masu ƙarfi da hatsari a gasar AFCON ta 2025, tare mai masaukin baƙi, Moroko.
Kocin Aljeriya, Vladimir Petković, ya yi fice wajen gina tawaga mai iya salon murza leda da hatsaru.
Ya tala leda da ’yan wasa da dama a wasannin rukuni, musamman a ɓangaren baya, amma duk da haka Aljeriya ta taka rawar gani.
A zagayen ’yan 16, Aljeriya ta samu nasara ne a mintunan ƙarshe ta hannun ɗan wasanta, Adil Boulbina, wanda ya zura ƙwallo, tare da taimakon Ramiz Zerrouki.
Petković ya ce ’yan wasansa sun san yadda za su jure wahala da kuma yin tsaya tsayin daka a filin wasa, abin da zai taimaka musu a wasan da za su fatata da Najeriya.
Baya ga ƙwarewa wajen tare hari, Aljeriya na da kyaftin ɗinta, Riyad Mahrez, wanda ya iya kai hare-hare masu hatsari a filin wasa.
Ana hasashen wasa tsakanin Najeriya da Aljeriya, zai zama ƙayatar duba da salon kowace ƙungiya a gasar AFCON ta bana.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link