Wang Yi Zai Ziyarci Habasha Da Somalia Da Tanzaniya Da Lesotho
Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar a yau Laraba cewa, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, zai ziyarci kasashen Habasha, da Somaliya, da Tanzaniya, da Lesotho, bisa gayyatar da ya samu, tsakanin raneku 7 zuwa 12 ga Janairun nan, kuma zai halarci bikin bude “Shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka”, a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU.
Wannan ce ziyarar farko cikin sabuwar shekarar nan ta 2026 da ministan harkokin wajen Sin zai gudanar a nahiyar Afirka, kuma irinta da ministan na Sin ke kaiwa kasashen nahiyar a duk farkon shekara cikin shekaru 36 a jere. (Amina Xu)