Harin Venezuela Ta’asa Ce Da Amurka Ke Tafkawa Tun Bayan Yakin Duniya Na Biyu
Ta’asar da Amurka ta tafka ta zuwa cikin Venezuela, kasa mai cin gashin kanta, ta cafke shugaban kasa mai cikakken iko da nufin gurfanar da shi a kotun kasarta, daya ne daga cikin munanan abubuwan da kasar take gadar wa duniya tun bayan yakin duniya na biyu.
Amurka ta yi kaurin suna wajen fakewa da guzuma ta harbi karsana a kasashe daban-daban a bayyane da kuma a boye, wadanda ake ganin sun yi hannun riga da manufofinta na ci da gumin wasu.
A shekarar 1953, hukumar leken asiri ta Amurka (CIA) ta mara baya ga kifar da firaministan Iran Mohammad Mossadegh bayan ya mayar da iko da arzikin man kasar zuwa ga kasarsa. Shekara guda bayan nan, hakan ya sake faruwa a Guatemala inda aka tumbuke zababben shugaban kasar Jacob Arbenz, dukka da sunan kare ’yancin jama’a.
A shekarar 1961, Amurka ta farmaki kasar Cuba, a 1983 kuma ta kai mamaya a kasar Grenada wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fito fili ta yi tir da hakan. Kazalika a 1989, ta kai hare-hare a Panama tare da tumbuke shugaban kasar Manuel Noriega bayan haddasa dimbin asarar rayukan fararen hula. Taho-taho har aka tsallako karni na 21, Amurka ba ta daina ta’asarta ba. Ta yi gaban kanta tare da wancakalar da dokokin kasa da kasa ta afka wa Iraqi a 2003, ta kuma zama kanwa-uwar-gamin wargaza kwanciyar hankalin Libiya a karkashin NATO a 2011. Wadannan duka wasu misalai ne kawai daga ta’asar da take tafkawa, baya ga yakin sunkuru na hana sakat a wasu kasashe.
Yanayin kasa da kasa ya riga ya shiga cikin wani mawuyacin hali da aka dade ba a ga irinsa ba sakamakon miyagun dabi’un Amurka, kuma galibi kamar yadda masharhanta da dama ke fada, ba don komai ba ne illa kare matsayinta na babakere a duniya. Harin da Amurka ta kai wa Venezuela ya kara tsananta fargabar al’umma a wasu yankuna da ake fama da rikice-rikice domin kar hakan ya zama silar murkushe kananan kasashen da ake rikici da su.
A daya daga cikin jawabansa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taba bayyana cewa, bai kamata a mayar da duniyarmu ta karni 21 mai wayewar kai ta dan’adam ta koma rayuwa irin ta namun daji ba, watau babba ya rika farautar mai rauni.
Hakika, lokaci ya yi da za a amsa kiraye-kirayen kasar Sin na hada karfi da karfe wajen tabbatar da bin dokokin kasa da kasa a karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya. Harin da Amurka ta kai wa Venezuela ya wuce wani abu na yankin Latin da Caribbean kawai, gargadi ne da an kararwa game da halin da duniya ke ciki na cin zalin daga kasar da ke ganin babu mai nuna mata isa. Yana gaya wa duniya cewa har yanzu za a iya yin hakan a kwana lafiya, kuma bin dokokin kasa da kasa ba tilas ba ne zabi ne ga manyan kasashe.
Idan abin ya ci gaba a haka ba tare da an ja masa burki ba, tsarin duniya da ke cikin mawuyacin hali zai iya rugujewa, musamman ma ganin cewa, bayan Venezuela, yanzu haka Amurka ta maida hankali ga kwace yankin Greenland na kasar Denmark, lamarin da zai sake haifar da mummunan rudani a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)