Idan ana neman ɗan siyasar da ba zai sayu da kuɗi ba, to ni ne — Kwankwaso
[ad_1]
Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya cewa bayyana babu wanda zai iya taya shi ko siyan sa da kuɗi a harkar siyasa.
Ya jaddada cewa ba shi da “farashi,” duk da cewa wasu na ganin kowane ɗan siyasa na da farashi.
Kwankwaso ya yi wannan bayani ne yayin da yake magana kan biyayya, cin amanar mutane, da siyasa a Najeriya, musamman a Jihar Kano.
Ya ce siyasa tana da nasara da kuma faɗuwa, sai dai ya yi gargaɗin cewa cin amanar mutane ya kan sa jama’a su yi fushi, musamman a lokacin da mutane da dama suka nuna rashin gamsuwa game da shugabanci.
“Rayuwa haka ta ke, har sai wani ya rasa wani zai samu. Tabbas, ya shiga tsarin da babu mafita. Da farko, mun san cewa cin amanar mutane babu kyau. Kowa ya san yadda jam’iyyar nan ke rasa amincewar mutane, musamman game da rashin tsaro da tattalin arziƙi,” in ji shi.
Ya bayyana cewa siyasar Kano ta bambanta da ta wasu sassan Najeriya, saboda masu kaɗa ƙuri’a suna da wayo a siyasance kuma ba sa sauƙin sha’ani wajen siyan su da kuɗi.
“Siyasar Kano a Najeriya ta bambanta. Idan ba a Kano ba, a ina za a haɗu da kai da jakar kuɗi a shiga taro tare da kai cewa za a ba ka abubuwa?” in ji shi.
Kwankwaso ya musanta batun cewa za a siyan dukkanin ’yan siyasa da kuɗi.
“Mutane sun saba cewa a Najeriya kowa na da farashi. Idan kana neman wanda ba shi da farashi, zo ka ga Rabiu Kwankwaso,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan da manufarsa kuɗi ne, da tuni ya sanya wa kansa farashi, amma babu wanda zai iya siye zuciyarsa.
Kwankwaso, ya kuma gargaɗi ’yan siyasa da masu kaɗa ƙuri’a da su guji yadda ake jan hankalinsu da kuɗi.
“Za ka sha wahalar shekaru huɗu, sai wata rana su zo su ba ka kuɗi kaɗan, sannan ka sake shan wahalar wasu shekaru huɗu,” in ji shi.
Ya yi kira ga ’yan siyasa da su tsaya kan ƙa’ida su yi aiki don amfanin mutane, inda ya bayyana cewa shugabancin da aka gina kan siye mutane da cin amanar mutane ba zai kawo ci gaba mai ma’ana ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link