’Yansanda Sun Ceto Yara 76 Da Aka Yi Safararsu A Kaduna
’Yansanda a Jihar Kaduna sun daƙile ayyukan masu safarar mutane tare da ceto yara 76 a yankin Kasuwan Magani.
Yaran, masu shekaru daga bakwai zuwa 20, ba su jikkata ko jin rauni ba.
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotu Ta Bayar Da Belin Malami, Matarsa Da Ɗansa Kan N1.5bn
- Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Sace Mutane A Taraba, Sun Ceto Mutane 3
’Yansanda sun ce sun ɗauki mataki ne bayan samun sahihan bayanai a ranar 5 ga watan Janairu, 2026.
Jami’an tsaro sun isa wajen, inda suka kama waɗanda ake zargi guda uku.
Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun kai yaran zuwa wasu sassan ƙasar nan domin yin aikatau.
A halin yanzu, waɗanda ake zargin na tsare a hannun ’yansanda, yayin da ake kula da lafiyar yaran tare da ƙoƙarin gano iyayensu.
’Yansanda sun ce suna ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.