Mun daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasa – Gwamnatin Burkina Faso

[ad_1]



Gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso ta ce ta dakile shirin kashe shugaban ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traore, da kuma shirin tayar da hankalin ƙasar.

Ministan tsaron ƙasar, Mahamadou Sana ne ya bayyana haka da safiyar Laraba.

Ya ce suna zargin tsohon shugaban kasar, Paul-Henri Damiba, wanda Captain Traore ya kifar da mulkinsa a shekarar 2022, da zama kanwa uwar gamin da ya kitsa shirin.

Ya ƙara da cewa an samu kuɗin shirya harin ne daga ƙasar Ivory Coast.

Babu wani jawabi daga Ivory Coast ko daga Laftanar Kanal Damiba kan lamarin.

An yi ƙoƙarin juyin mulki sau da dama a kan Kyaftin Traore, inda gwamnati ke zargin Ivory Coast da hannu a ciki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *