Sin Ta Bukaci Duniya Ta Sa-ido Kan Aniyar Japan Ta Yin Kwaskwarima Ga Takardunta Na Tsaro

[ad_1]

Aniyar Japan ta yin kwaskwarima ga takardunta na tsaron kasa guda uku ta nuna matakan da take dauka masu hatsari na hanzarta sake bude fagen amfani da karfin soji, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Talata, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su sa-ido sosai.

Mao Ning ta yi wannan tsokaci ne a martanin da ta mayar kan kalaman da firaministar Japan Sanae Takaichi ta yi kwanan nan cewa, za a ci gaba da tattaunawa game da hakan don cimma burin sake fasalin takardun tsaron kasa guda uku a cikin shekarar.

Kazalika, duk dai a yau Talata, ma’aikatar kasuwanci ta sanar da cewa, kasar Sin ta yanke shawarar karfafa dakile fitar da kayayyaki da ake iya amfani da su ta fuskoki biyu zuwa Japan, tun daga ranar Talatar.

Ma’aikatar ta ce kungiyoyi ko daidaikun mutane daga kowace kasa ko yanki da suka karya wannan doka ta hanyar kaiwa ko samar da kayayyakin da ake iya amfani da su ta fuskoki biyu wadanda asali a kasar Sin aka kera su, zuwa ga kungiyoyi ko daidaikun mutane a Japan, za a tuhume su bisa doka.

Ma’aikatar ta ce an yanke wannan shawara ce bisa ga dokoki da ka’idoji na kasar Sin a kan kare tsaron kasa da muradun kasa da kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na huldar kasa da kasa kamar hana yaduwar makamai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *