Yawan Fasinjojin Jiragen Sama A Sin Ya Kai Matsayin Koli A Duniya

[ad_1]

Hukumar lura da zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2025 da ta gabata, yawan fasinjoji da aka yi jigilarsu ta jiragen sama a Sin ya kai miliyan 770, adadin da ya karu da kaso 5.5 bisa dari, yayin da na kayayyaki da wasiku da aka yi jigilarsu ya kai tan miliyan 10 da dubu 172, adadin da ya karu da kashi 13.3 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.

Daga cikin wadannan adadi, jiragen sama na kasa da kasa sun dawo da zirga-zirga da sama da kaso 90 bisa dari kan na shekarar 2019, kana sufurin fasinjojin kasa da kasa ya karu da kaso 21.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2024.

Har ila yau, karfin jigilar fasinjoji ta jiragen sama ya kai kashi 39 bisa dari, a cikin jimillar tsarin sufurin kasar, yayin da yawan mutanen da ke amfani da jiragen sama ya wuce miliyan 500, matakin da ya sa yawan fasinjojin Sin dake zirga-zirga ta jiragen sama ya kai matsayin koli a duniya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *