’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Daga Cikin Likitoci 2 Da Suka Sace A Edo


Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ɗaya daga cikin likitocin biyu da suka sace a Jihar Edo.

Mamacin, Tahir Abu Emhoye, an sace shi tare da ɗan uwansa a ranar 1 ga watan Janairu, 2026, a garin Auchi.

  • Sakataren APC Ya Buƙaci Murabus Ɗin Wike Saboda “Tsoma Baki” A Harkokin Jam’iyya
  • Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Manyan Kasashe Da Su Jagoranci Biyayya Ga Yarjejeniyar Kafuwar MDD

An sace ’yan uwan ne da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a titin City Pride Road, kusa da gidansu, yayin da suke dawowa daga aiki.

Tahir sabon likita ne da ya kammala karatu a Jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma, yayin da babban yayansa ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Edo da ke Auchi.

Daga bisani, masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalinsu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 200 kafin sakin su.

Rahotanni sun ce an kashe Tahir sannan aka jefar da gawarsa a bakin wani kogi.

Jami’an tsaro ne suka gano gawar yayin da suke binciken dazuka a yankin domin ceto waɗanda aka sace.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an gano gawar a bakin kogi, kuma iyalan mamacin sun tabbatar da cewa ɗaya ne daga cikin mutanen da aka sace.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *