Xi Jinping ya taya jagoran mulkin sojin Guinea murnar lashe zaɓe

[ad_1]



Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, ya taya jagoran mulkin sojin Guinea, Mamady Doumbouya, murnar nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnatin China suka ruwaito a ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Kotun Ƙoli ta Guinea ta tabbatar da gagarumar nasarar da Doumbouya ya samu a zaɓen da aka gudanar a ranar 28 ga Disamba, inda ya lashe kashi 86.72 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Zaɓen dai ya gudana ne ba tare da manyan ‘yan adawa sun shiga takara ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na China, Xinhua, ya ruwaito cewa Shugaba Xi ya aike wa Doumbouya da saƙon taya murna a ranar Lahadi.

A cewar rahoton, Xi Jinping ya ce China da Guinea sun daɗe suna gina alaƙa bisa girmama juna, daidaito da kuma moriyar juna.

Shugaban na China ya ƙara da cewa yana ba da muhimmanci sosai ga bunƙasar alaƙar China da Guinea, tare da nuna shirinsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Doumbouya domin ƙara bunƙasa haɗin gwiwar dabarun ƙasashen biyu.

Muhimmancin Guinea ga China

Ƙasar Guinea mai al’umma fiye da miliyan 14 wadda ke yammacin Afirka, na ƙarƙashin mulkin Doumbouya tun bayan juyin mulkin da ya yi a shekarar 2021.

Ƙasar na da dimbin albarkatun ma’adinai, musamman bauxite, wani dutse mai ɗauke da sinadarin aluminium, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga masana’antu.

Bayanan hukumar kwastam ta China sun nuna cewa daga cikin yuan biliyan 105 (kimanin dala biliyan 15.1) na bauxite da makamantansa da China ta shigo da su daga Janairu zuwa Nuwamban bara, kashi 76 cikin 100 daga Guinea ne.

Baya ga haka, kamfanonin China na taka rawa sosai a babban aikin haƙar ma’adinai na Simandou, wanda ake sa ran zai sauya fasalin tattalin arzikin Guinea tare da mayar da ita ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya wajen fitar da ma’adinan irin karfe.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *