Xi Ya Taya Doumbouya Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Guinea
[ad_1]
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Mamady Doumbouya bisa zabensa a matsayin shugaban kasar Guinea.
A cikin sakon nasa wanda aka aike ranar Lahadi, Xi ya bayyana cewa Guinea ita ce kasa ta farko a yankin kudu da hamadar Sahara da ta kulla huldar diflomasiyya da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.
Ya ce, bangarorin biyu sun dade suna girmama juna, bisa daidaito da kuma cin gajiyar juna, kana suna goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi manyan muradunsu da kuma manyan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya, sannan sun gudanar da hadin gwiwa mai alfanu domin samun ci gaba na bai-daya.
Kazalika, Xi ya kuma ce yana mai da hankali sosai kan yaukaka zumuncin Sin da Guinea, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Doumbouya don kara habaka cikakkiyar dangantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, domin ba da gudummawa mai girma wajen inganta jin dadin al’ummomin kasashen biyu da kuma karfafa nuna goyon baya a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link