AFCON 2025: Morocco, Senegal Da Mali Sun Tsallaka Zuwa Zagayen Kwata Fainal


A ci gaba da gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afrika (AFCON 2025) da ke gudana a ƙasar Morocco, ƙasashe uku Senegal, da Mali da kuma Morocco sun samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen Kwata Fainal bayan cin nasarori a wasannin zagayen ƴan 16. Senegal ce ta fara kaiwa wannan mataki bayan doke Sudan da ci 3-1 a wasan da suka buga ranar Asabar.

A wani wasan da aka buga a ranar Asabar, Mali ta fitar da kasar Tunisia ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga, duk da cewa ƴan wasan Mali sun buga ragowar wasan da ɗan wasa daya ƙasa bayan an ba su jan kati. Haka kuma, a wasan da aka buga yammacin Lahadi, ƙasar Morocco mai masaukin baki ta doke Tanzania da ci 1-0, inda dan wasan Real Madrid, Brahim Diaz, ya zura ƙwallon daya tilo da ta ba su tikitin zuwa Kwata Fainal.

  • AFCON 2025: Yadda Wasannin Zagayen ‘Yan 16 Za Su Kasance
  • AFCON 2025: Zan Taimaka Wa Uganda Ta Doke Super Eagles Duk Da Mahaifina Ɗan Nijeriya Ne – Ikpeazu

Brahim Diaz ya ƙara kafewa a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar bana, bayan kai ƙwallon slla ta huɗu. Wannan nasara ta sa ya zama dan ƙasar Morocco na farko da ya zura ƙwallo a wasanni huɗu a jere a tarihin gasar AFCON, lamarin da ya ƙara daga darajarsa a idon masoya ƙwallon ƙafa.

A wasannin zagayen Kwata Fainal da za a buga nan gaba kaɗan, Senegal za ta kara da Mali, yayin da Morocco za ta fafata da daya daga cikin ƙasashen Kamaru ko Afirka ta Kudu. Sauran wasannin zagayen ƴan 16 da ke tafe sun haɗa da Nijeriya da za ta kara da Mozambique, sai kuma Masar da za ta fafata da Benin.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *