Dalilin Ɗage Sauya Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa 12 Ga Janairu


Rahotannin da ke nuni da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC sun samu sabon sauyi, bayan da aka ɗage ranar sauya sheƙar, kamar yadda jaridar PlatinumPost ta rawaito.

Majiyoyi masu kusanci da gwamnan sun bayyana cewa ranar da aka fara tsarawa domin sanar da sauyin sheƙar a hukumance wato Litinin, 5 ga Janairu, 2026 yanzu an sauya ta zuwa Litinin, 12 ga Janairu, 2026.

  • Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Wa Da Bappa Bichi Martani
  • Komawar Abba APC: Maslahar Al’umma Ko Kasuwar Bukata?

A baya dai, jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a ranar 5 ga Janairu, lamarin da ya jawo cece-kuce a fagen siyasar Kano da ƙasa baki ɗaya.

Sai dai wata majiya mai tushe, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa gwamnan ya nemi ƙarin lokaci ne domin kammala tuntuɓa. Majiyar ta ce ta halarci wani taro da aka gudanar tsakanin Gwamna Yusuf da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Abuja ranar Juma’a.

Daily Nigeria ta rawaito yau cewa, Gwamna Yusuf na son ci gaba da tuntuɓar wasu ƴan majalisar dokokin jihar Kano da sauran manyan masu ruwa da tsaki, musamman waɗanda har yanzu ba su bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan yunƙurin siyasa ba.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *