Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

[ad_1]



Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.

Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne da rundunar California Army National Guard, mai dakaru sama da 18,000.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda Aminiya ta tabbatar, Isah ya mayar da martani kan jita-jitar cewa Amurka za ta ɗauki matakin yaƙi a kan Najeriya saboda zargin yi wa Kiristoci kisan gilla.

Ya bayyana cewa ba zai taɓa amfani da makami a kan mutanensa ba.

“Ba zan shiga Najeriya na kashe iyayena ba saboda ƙaryar cewa ana kashe Kiristoci,” in ji shi.

Ya ce duk da yake yana Allah-wadai da kashe-kashe da tashin hankali, bai kamata matsalar tsaro a Najeriya a danganta da wani addini ba.

“Ba zan ƙaryata batun kisan Kiristoci da Musulmai ba,” in ji shi.

“Shekau, Bello Turji, Dogo Gide da sauransu ba suna kai wa wani addini ɗaya hari ba ne kaɗai.”

Maganganun Isah na zuwa ne daidai lokacin Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi a kan Najeriya.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ba ta addini ba ce, inda ta ce matsalar na shafar Musulmai da Kiristoci baki ɗaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *