DSS Ta Cafke Wanda Ya Yi Garkuwa Gami Da Kashe Wata Farfesa A 2023
Daga Rabiu Ali Indabawa
Jami’an Hukumar Tsaron Farin kaya (DSS) sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, wadanda ake danganta su da sacewa da kashe wata farfesa a fannin ilimin jijiyoyin kwakwalwa, Ekanem Philip-Ephraim, a Jihar Cross Riber a shekarar 2023.
An sace Philip-Ephraim ne a ranar 13 ga Yulin 2023 a ofishinta da ke Calabar, Jihar Cross Riber, daga bisani kuma aka tabbatar cewa masu garkuwar sun kashe ta.
- Batutuwan Da Suka Ci Wa ‘Yan Adawa Tuwo A Ƙwarya A Siyasar 2025
- Sama Da Kwantainoni 600 Ke Sauka Duk Wata A Defo Din Kano —Mahukunta
A cewar tsohon Shugaban Kungiyar Likitocin Nijeriya (NMA) reshen Jihar Cross Riber, Dakta Felid Archibong, masu garkuwar sun boye kansu a matsayin marasa lafiya ne, kuma yayin da take duba su, sai suka fito da makamai suka yi awon gaba da ita da misalin karfe 7:15 na yamma.
Sacewarta ta sa reshen NMA na jihar ya janye ayyukan lafiya a matsayin zanga-zanga, inda suka bukaci a ceto ta.
Jami’an DSS da suka yi magana a ranar Litinin bisa sharadin a sakaya sunansu, sun bayyana cewa an kama wadanda ake zargin wanda aka bayyana su a matsayin shugaban gungun masu laifi mai shekaru 23, Patrick Essien Etim, da kuma Bassey Antiha Asukuo mai shekaru 40 ne a ranar 27 ga Disamba a wani asibiti a jihar, yayin da ake zargin suna shirin sace wani babban likita.
Daya daga cikin jami’an ya ce DSS na bibiyi gungun tun daga Yulin 2023, lokacin da wasu ’yan bindiga da suka boye kansu a matsayin marasa lafiya suka sace Philip-Ephraim a asibitinta mai zaman kansa da ke hanyar Atimbo, Calabar.
“Jami’anmu, a ranar 27 ga Disamba, sun kama shugaban gungun da wani wanda ake zargi da sacewa da kashe wata fitacciyar farfesa a fannin ilimin jijiyoyin kwakwalwa, Ekanem Philip-Ephraim, a shekarar 2023.
“Shugaban gungun, Patrick Essien Etim mai shekaru 23, da abokin aikinsa, Bassey Antiha Asukuo mai shekaru 40, an cafke su a wani asibiti a Jihar Cross Riber.
“Mutanen biyu sun amsa laifin, inda suka bayyana cewa sun kashe farfesar bayan sun karbi kudaden fansa daga daya daga cikin iyalinta.”
“Shekaru biyu kenan na azaba ga ’yan uwanta da masoyanta, suna cikin rashin sanin abin da ya faru da farfesar. Ina ganin da wannan kamun, iyalinta da masoyanta za su samu nutsuwa a karshe da kuma rufewar zuciya da suka dace,” in ji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa wadanda ake zargin sun kuma amsa sace wasu mutane tare da lalata wayoyin wutar lantarki.
Wani wanda ake zargi, mai suna Isaac Ekpeyong, shima jami’an DSS sun kama shi.
A cewar majiyar, wadannan kamun suna nuna kokarin DSS na ci gaba da tarwatsa cibiyoyin aikata laifuka da kuma kara tabbatar da tsaron al’umma.
“Wannan gagarumar nasara na nuna jajircewar DSS wajen komawa yin ayyukanta na boye da kuma dawo da tsaron jama’a a fadin kasar,” in ji majiyar.