NNPP ta rushe shugabancinta a Kano, za ta naɗa shugabancin wucin gadi

[ad_1]



Uwar jam’iyyar NNPP ta rushe kafatanin shugabanninta na mazaɓu, ƙananan hukumomi da kuma matakin jiha.

Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar na Ƙasa (NWC) ne, ya yanke wannan hukunci bayan taron gaggawa da aka yi a Abuja.

Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da dokokin jam’iyyar.

Jam’iyyar za ta naɗa kwamitin wucin gadi domin kula da harkokin jam’iyyar a Jihar Kano, har sai an bayyana mataki na gaba.

Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta a Kano, ciki har da rikicin shugabanci.

Jam’iyyar ta gode wa tsofaffin shugabannin bisa gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa jam’iyyar a jihar.

Sannan ta roƙi mambobinta su zauna lafiya, su ci gaba da mara mata baya yayin da jam’iyyar ke sake tsara shugabancinta a Kano.

Wannan dai duk na zuwa ne bayan raɗe-raɗin da ake yi ka cewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin raba gari da ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da komawa jam’iyyar APC.

Wannan lamari ya sake haifar da ruɗani a jam’iyyar, lamarin da ya sanya wani tsagi dakatar da shugaban jam’iyyar, Hashim Dungurawa tare da naɗa Abdullahi Ajiya a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *