Buƙatar A Sake Duba Sabuwar Dokar Haraji

[ad_1]

A makon da ya gabata ne, a shiga cikin wata zazzafar dambawar ka’addama kan zargin cushen a cikin dokokin harji na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wadda gwamnatinsa, ta gabatarwa da ‘yan majalisar kasar, ta kuma zamo doka.

Akasarin masu bibiyar lamarin, tun daga matakin farko na fara tsara kunkurin kafin ya zama doka.

Kundurin harajin sun zamo daka ne, biyo bayan faman tuntuba da aka ta hakilon yi, wanda kuma ake ta ci gaba da yin koarafi a kasar cewa, an dibga cushe a cikin dokokin na harajin, wadanda ‘yan majalisar suka amince da su.

A yanzu haka dai, ana ganin akwai matukar bukatar a gudanar da cikakken bincike, kan batun zargin cushen da aka yi, a cikin dokikin harajin.

A watan Fabirairun 2025 ne, Majalisar Wakilai ta amince da dokokkin harin bayan gudanar da tarukan jin ra’ayoyin jama da kuma yin dubi kan wasu batun da za su iya janyo koma baya ga dokokin, wadanda daga baya, aka hade dokokin da sauran da Majalisar Dattawa, ta amince.

Dokokin guda hudu sun hada da, dokar haraji ta kasa da dokar haraji ta bangaren mulki da dokar haraji ta tara kudaden shiga da kuma dokar haraji ta hadaka ta hukumar tara haraji.

Shugaba Bola Tinubu ne, ya rattaba hannun kan wadannan dokokin a watan Yunin 2025, bisa nufin samar da sauye-sauye a tsarin tara haraji na kasa.

Sai dai, an tsara wadannan dokikin harajin, za su fara aiki ne gadan-gadana a watan Janairun 2026.

Amma sai wata takaddama ta kunno kai a tsakanin majalisar kasa bisa zargin da wasu ‘yan Majalisar Wakilai suka bijro da shin a cewa, an yin cushe, a cikin wadannan dokokin harajin tare da kuma wani zargin da wasu ‘yan kasar suka yi, na yin cushen.

Dan Majalisar Wakilai da ya fara bijiro da zargin cushen shi ne, Abdulsamad Dasuki, wanda ya sanar da cewa, dokokin harjin, sun saba da wadanda wanda ‘yan Majalisar suka amince da su, aka kuma gabatarwa da alummar kasa.

A cewarsa, wannan cushen ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan da kuma dokokin kasar, kuma bai kamata Majalisar, ta yi sako-sako kan batun ba.

Sai dai, a martanin da Shugaban Majalisar Wakilai In response, Abbas Tajudeen, ya bayar da tabbacin cewa, Majalisar za ta dauki matakan da suka dace domin lalubo da mafita, kan batun.

Domin tabbatar da wannan alawashin na Abbas ne, ya sanya Majalisar ta kafa wani kwamiti na wucin gadi, mai mutane bakwai domin gudanar da bincike kan wannan batun na cushen.

Kwamtin a karkashin shugabancin dan Majalisa Aliyu Betara, ana sa ran zai kammala bincikensa ya kuma gabatar da rahoton sa a gaban Majalisar, nan da mako daya.

Wannan Jaridar na shawartar kwamitin da ya gudanar da aikinsa, ba tare da an yi masa, wani katsalandan ba kuma ba tare da sanya wata siyasa ba, ya kuma tabbatar da ya sanar da ‘yan Nijeriya binciken da ya gudanar.

Hakan ne, kawai zai sanya yakini da yarda, a cikin Zuciyoyin ‘yan kasar nan.

Kazalika, akwai matukar bukatar kwamtin ya gudanar da binciken sa, bisa ka’ida da kuma gaskiya.

Dole ne kuma bangaren zartarwa ya bari dokar kasa ta yi aikinta, yadda ya dace, musamman ba wai kawai domin zargin cushen ba, amma domin a kawar dukkan wani shakku daga cikin Zuciyar ‘yan kasar kan zargin batun na cushen.

Bugu da kari, abinda ya zarce batun kara samar da kudaden shiga da kuma kara tara harji ga kasar, doka za ta yi aikinta, wanda hakan zai kuma kara farkar da ‘yan Nijeriya, kan irin kudaden da Gwamnatin ke kashewa da tare da kuma tabbatar da tana bin ka’ida, wajen kashe kudaden.

Akwai bukatar a rinka tafiyar da komai yadda ya dace a kasar nan, duba da cewa, daukacin dokokin kasar, ba wai sune, suka kirkiri kansu da kansu ba.

Daukacin sabuntawar da za a yi domin tabbatar da inganci da kuma yin abinda ya dace, abu ne, da ba za a iya yin watsi, da hakan ba.

Dole ne dai, dokar ta faro daga wani wuri, wanda kuma aka tsar za fara fara wanzar da ita, gadan-gadan a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2026.

A bisa ra’ayin mu, fara yin gwajin wadannan dokokin harjin a cikin kasa, zai tabbatar da saurin gudanar da garanbawul.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *