Bankwana Da 2025: Kaunar Kasar Sin Ga Zaman Lafiyar Duniya Da Kiyaye Martabar Yankunanta

[ad_1]

A shekarar 2025 da muke bankwana da ita a yau, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin samar da zaman lafiya a duniya, ta hanyoyin diflomasiyya, kawo ci gaba, da inganta huldar mabambantan bangarori a daidai lokacin da rikice-rikicen kasa da kasa suka tsananta zuwa wani mataki da ba a ga irinsa a shekaru da dama ba.

Domin karfafa aza harsashin gina zaman lafiya mai dorewa, Sin ta gabatar da muhimman shawarwari ga duniya da suka kunshi: Shawarar Inganta Tsaron Duniya, da Shawarar Tsarin Ciyar Da Duniya Gaba, da Shirin Bunkasa Wayewar Kai A Duniya, da kuma Sabon Tsarin Inganta Jagorancin Duniya. Dukkan wadannan sun kawo muhimman dabaru na magance rikice-rikice daga tushe, daga bangaren rashin daidaito zuwa gibin shugabanci, kuma sun yi daidai da muhimman abubuwan da Majalisar Dinkin Duniya ta sa a gaba.

A cikin shekarar 2025, kasar Sin ta ba da karfi ga jaddada hadin gwiwar kasashe maimakon fito-na-fito. Kiran da Shugaba Xi Jinping ya yi ta maimaitawa na samar da tsaro na bai-daya da nuna adawa da siyasar danne wata kasa ya yi tasiri a duk fadin kasashe masu tasowa, wadanda suka kara samun damar fada-a-ji bisa goyon bayan babbar alakar diflomasiyya ta kasar Sin a duniya da kuma shiga a dama da su cikin harkokin yanki da na duniya baki daya.

Rawar da kasar Sin ta taka a MDD kan dakatar da yakin Zirin Gaza, da kokarin ganin an sulhunta rikice-rikicen kasashe irin su Sudan, da Sudan ta Kudu, da Syria da kuma na baya-bayan nan tsakanin Cambodia da Thailand, duka sun nuna kaunarta ga zaman lafiya. Haka nan ta yi yekuwar tunatar da duniya muhimmancin kiyaye zaman lafiya, ta hanyar gudanar da bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da mamayar dakarun Japan da kuma yakin duniya na biyu.

Sai dai kuma, duk da kokarinta na tabbatar da dorewar zaman lafiyar duniya, zuwa karshen 2025, masu tsokanar fada kan batun Taiwan suna kokarin sake tayar da zaune tsaye, wadda kuma Sin ta nuna ba za ta bari wani ya zo har cikin gida ya yi mata sakiyar da ba ruwa ba.

Sin ta yi amannar cewa, samun daumammen zaman lafiya na bukatar kare ’yancin kasa da kiyaye martabar yankunanta. Ta sha damarar mayar da martani mai gauni a kan ayyukan wuce gona da iri na ‘yan awaren Taiwan, tare da ’yan katsalandan da ke mara musu baya daga waje.

Atisayenta na soja a kwanan nan da kuma gargadinta mai karfi ta hanyar diflomasiyya ba abubuwa ne da suka saba wa yanayin zaman lafiyar duniya ba, sai dai matakai ne da suka wajaba ta dauka don hana fadada barazana da kuma tabbatar da ka’idar “Sin daya tilo a duniya”. Kazalika, ta dauki batun habaka zaman lafiya a duniya da kuma kare ’yancin martabatar yankunanta a matsayin wani nauyi da ba zai yiwu a raba su wajen saukewa ba. Kuma hakan ya tabbatar da tabarau da ta sa na “kifi na ganinka mai jar koma!” Da fatan ’yan tayar da zaune tsaye sun fahimci sakon kuma za su bari a shiga sabuwar shekarar 2026 cikin salama! (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *