Kakakin Babban Yankin Sin: Atisayen PLA Gargadi Ne Ga Masu Fafutukar “’Yancin Kan Taiwan” Da ’yan katsalandan na waje

[ad_1]

LAtisayen soja na baya-bayan nan da rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) ta gudanar a kusa da tsibirin Taiwan, gargadi ne mai tsanani ga ‘yan aware masu neman “’yancin kan Taiwan” da kuma ’yan katsalandan daga waje, kamar yadda wata mai magana da yawun babban yankin kasar Sin ta bayyana a yau Laraba.

Da take jawabi a wani taron manema labarai, mai magana da yawun ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar, Zhang Han ta bayyana cewa, gudanar da atisayen ya zama wajibi kuma mataki ne na kare mulkin kan kasa da kiyaye martabar yankunanta.

Zhang ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da take amsa wata tambaya da ‘yan jarida suka yi mata game da atisayen da aka yi wa lakabi da “Kudurin adalci na shekarar 2025” a tsibirin Taiwan, wanda rundunonin PLA da ke karkashin reshenta na gabashi suka gudanar a ranakun Litinin da Talata da suka gabata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *