Haraji: Kotu ta ƙi dakatar da fara aiwatarwa a ranar 1 ga Janairun 2026




Wata Babbar Kotun Tarayya, ta ƙi amincewa da buƙatar dakatar da fara aiwatar da sabbin dokokin haraji da za su fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

Wata ƙungiya mai suna African Initiative for Abuse of Public Trust ce, ta shigar da ƙara, inda ta nemi kotu ta hana aiwatar da dokokin harajin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya sanya wa hannu.

A hukuncin da ya yanke a ranar 30 ga watan Disamba, 2025, Mai shari’a Kawu Bello, ya ce kotu ba ta da ikon dakatar da aiwatar da dokokin da aka riga aka amince tare da wallafa su a hukumance, sai dai idan akwai ƙwararan hujjojin da ke nuna an aikata laifi.

Alƙalin, ya ƙara da cewa Majalisar Tarayya ce kawai ke da alhakin soke irin waɗannan dokoki ko kuma kotu ta soke wasu sassa bayan sauraron ƙara.

Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin cewa Dokar Haraji ta 2025 da sauran dokoki masu alaƙa da su, za su fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

Kotun ta kuma ce za su ci gaba da aiki har sai an yanke hukunci a kan shari’ar.

Daga bisani alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 9 ga watan Janairu, 2026.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *