Me Ya Sa Kasar Sin Ta Jawo Hankulan Masu Zuba Jari Daga Kasashen Waje A 2025?
[ad_1]
A shekarar 2025, saka hannun jari daga kasashen waje ya ci gaba da karuwa a kasar Sin. Wakilan CMG sun tattauna da kusan shugabannin kamfanoni dari na kasashen duniya, kuma “kirkire-kirkire” sun kasance jigon abubuwan da suka fito daga bakinsu. Hermann Simon, wanda aka ba shugabanci na girmamawa a kamfanin Verband Deutscher Hidden Champions (VDHC), ya ce, “Na zo kasar Sin kusan sau 75, kuma akwai kirkire-kirkire a ko ina a nan.”
A shekarar 2025, manufofin gwamnatin kasar Sin sun ba da tabbaci sosai ga masu jari na kasashen waje wajen cin gajiyar kasar Sin, wanda hakan ya nuna kudurin kasar Sin na bude kofa. Shugaban kamfanin Mercedes Benz, Ola Källenius, ya ce, “Gwamnatin kasar Sin ta nuna wata babbar alama cewa kasar tana bude kofa ga kasashen waje, kuma za ka iya amincewa da kasar Sin.”
Shekarar 2026 ita ce shekarar fara aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na raya ci gaban kasar Sin karo na 15, kuma masu zuba jarin kasashen waje na fatan cin moriyar damammaki tare da kasar Sin. Sandeep Seth, babban jami’in bunkasa ci gaban kamfanin Tapestry kuma shugaban sashen kasa da kasa na kamfanin, ya yi nuni da cewa a cikin sabon shirin shekaru biyar-biyar, gwamnatin kasar Sin ta ba da shawarar habaka sayayya sosai, musamman bisa dogaro da mutane masu matsakaicin samun kudin shiga, wadda hakan ya dace sosai da matsayin kamfanin Coach and Tapestry. Kana ya kara da cewa, “Za mu yi amfani da wannan damar gaba daya kuma mu ci gaba da kara zuba jari a kasar Sin.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link