Shugaba Xi Zai Gabatar Da Sakon Murnar Sabuwar Shekarar 2026
[ad_1]
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da sakon sabuwar shekara da misalin karfe 7 na yamma a ranar Laraba domin maraba da shigowar shekarar 2026.
Za a watsa jawabin sakon nasa ta manyan tashoshin talabijin da rediyo na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), da shafukan intanet da na sada zumunta na manyan kafofin watsa labarai, ciki har da na jaridar People’s Daily da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link