An Kashe Mutane 8 A Wasu Sabbin Hare-hare A Kebbi, ‘Yansanda Sun Fara Bincike


Mutane takwas sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da wasu ’yan bindiga suka kai ƙauyukan Kaiwa, Gelawu da Gebbe da ke Ƙaramar Hukumar Shanga a Jihar Kebbi.

Rundunar ’Yansandan Jihar Kebbi ta ce hare-haren sun jefa jama’a cikin fargaba tare da tilasta wa mutane da dama tserewa domin tsira da rayukansu.

  • Sin Za Ta Kyautata Tsarin Lura Da Kudin Kasar Na Dijital A Shekara Mai Kamawa
  • Shugaban Ƙaramar Hukumar Yusfari Abba Aji, Ya Rasu

Kakakin rundunar, Bashir Usman, ya tabbatar da cewa mutane bakwai sun mutu a yayin hare-haren, yayin da wani mutum ɗaya ya rasu daga baya a asibiti.

Ya ƙara da cewa mutum guda na ci gaba da karɓar kulawar likitoci.

Ya ce jami’an tsaro sun fara bincike a yankin tare da ƙara sintiri domin hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare.

Mazauna yankin sun bayyana hare-haren a matsayin abin firgici, inda suka ce yankunan ba su taɓa fuskantar irin wannan tashin hankali ba tsawon shekaru da dama.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *