’Yan Jaridar NTA 7 Sun Rasu A Hatsarin Motar A Hanyar Gombe–Yola

[ad_1]

’Yan jarida bakwai sun rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Gombe zuwa Yola da yammacin ranar Litinin.

Waɗanda abin ya shafa mambobi ne na Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), reshen Jihar Gombe, inda suke tafiya a cikin motar NUJ.

  • Ɗaliban Nijeriya Sun Nemi A Dakatar Da Dokor Haraji
  • Mutane 4 Sun Rasu Bayan Motoci Sun Kutsa Cikin Gasar Al’adun Eggon A Nasarawa

Rahotanni sun nuna cewa suna dawowa ne daga ɗaurin aure da aka shirya domin taya wani abokin aikinsu murna wanda ke aiki da Hukumar Talabijin ta Ƙasa (NTA).

Shida daga cikin waɗanda suka mutu ma’aikatan NTA ne a Gombe, yayin da ɗaya kuma ma’aikacin StarTimes ne.

Waɗanda suka jikkata na karɓar kulawar likitoci a asibitoci daban-daban a jihar.

Lamarin ya jefa ‘yan jarida a Gombe cikin jimami, inda abokan aiki da jama’a ke nuna alhini da kaɗuwa kan al’amarin.

Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Gombe ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan musabbabin faruwar hatsarin ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *