An Sanar Da Kananan Dandaloli Hudu Na Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na 2026 Na CMG
[ad_1]
A yau Lahadi ne aka sanar da kananan dandaloli hudu na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa ta shekarar 2026, na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, wadanda ke cikin birnin Harbin na lardin Heilongjiang, da birnin Yiwu na lardin Zhejiang, da birnin Hefei na lardin Anhui, da kuma birnin Yibin na lardin Sichuan. Kananan dandalolin za su samar da shirye-shirye na bikin bazara, dake nuna al’adun gargajiyar Sinawa, tare da babban dandali dake cikin birnin Beijing.
Shugabannin hukumomin da abin ya shafa na CMG, da na kananan dandalolin hudu, na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na 2026, da wakilan tawagar dake jagorantar shirye-shiryen da sauransu, sun halarci taron da aka gudanar a yau Lahadi. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link