’Yan bindiga na neman N42m kafin sakin ’yan maulidi 28 da suka sace a Filato




’Yan bindigar da suka sace matafiya 28 a Jihar Filato, sun jaddada buƙatar biyan Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum.

An sace matafiyan, waɗanda suka haɗa da maza, mata da yara, a ranar Lahadin da ta gabata a ƙauyen Zak da ke gundumar Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase.

Matafiyan na kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Sabon Layi domin halartar maulidi, sai ’yan bindiga suka tare motarsu suka yi awon gaba da su.

’Yan uwan waɗanda aka sace sun ce ’yan bindigar sun fara kiransu a ranar Talata, inda suka buƙaci Naira miliyan 1.5 miliyan kan kowane mutum.

Iyalan nasu sun roƙe su da su rage kuɗin, inda suka bayyana musu cewa ba su da halin biyan wannan adadi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Wase, Muhammad Hamisu, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun tura sojoji da jiragen sama masu saukar ungulu domin bincike da ceton mutanen.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, ta kuma tabbatar da cewa an tura tawagar jami’an bincike zuwa yankin domin ceto matafiyan da kuma cafke waɗanda suka aikata laifin.

Sai dai wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Ibrahim Musa, ya ce ’yan bindigar sun sake kiransu a ranar Lahadi, inda suka sake jaddada buƙatarsu.

“Sun ce sun ga jiragen sama na shawagi suna neman inda ake tsare da mutanen, amma ba za su sake su ba sai an biya kuɗin fansa.”

Har yanzu dai ’yan uwan matafiyan na ci gaba da roƙon ’yan bindigar da su saki ’yan uwan nasu, inda suka ce ba su da halin haɗa kuɗin da suke nema.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *