Tsayin Layukan Dogo Na Jirage Masu Saurin Tafiya Na Kasar Sin Ya Kai Kilomita 50,000

[ad_1]

Kasar Sin wadda ke kan gaba a duniya ta fuskar tsayin layukan dogo na jiragen kasa masu matukar gudu, ta yi nasarar fadada tsayin wadannan layukan dogo zuwa sama da kilomita 50,000, bayan da ta kaddamar da wani sabon layin sufurin jiragen kasan masu saurin gaske.

Da safiyar yau Juma’a ne jirgin kasa mai matukar sauri samfurin “Fuxing”, ya bar tasharsa dake birnin Yan’an na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar ta Sin zuwa birnin Xi’an, a wani mataki na kaddamar da sabon layin.

An tsara layin dogo na Xi’an zuwa Yan’an, ta yadda jiragen kasa dake zirga-zirga a kan sa za su iya gudun da zai iya kaiwa har kilomita 350 a duk sa’a, ta yadda zai rage lokacin tafiya tsakanin biranen biyu da kusan sa’a guda.

Tun a shekarar 2008 ne aka kaddamar da sufuri ta amfani da jiragen kasa masu matukar sauri a kasar Sin, inda a lokacin aka bude layin birnin Beijing zuwa Tianjin. Daga lokacin ne kuma aka ci gaba da fadada layukan, zuwa adadin da ya haura na daukacin wanda sauran kasashen duniya suke da shi. Kazalika, a halin yanzu kasar Sin na kan gaba wajen aiwatar da tsarin sufurin kasuwa na jiragen kasa masu matukar saurin tafiya a duniya.

A cewar kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin, cikin tanadin manufar raya kasa ta shekaru biyar-biyar karo na 14 da aka aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, Sin ta gina, tare da fara amfani da karin layukan dogo na rukunin jiragen masu saurin tafiya da ya kai kilomita 12,000. Ya zuwa yanzu, jiragen kasa masu sauri suna sufuri a kaso 97 bisa dari na jimillar birane kasar Sin dake da yawan jama’a da ya haura 500,000. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *