GORON JUMA’A

[ad_1]

Jama’a barkanmu da juma’a, barkanmu da kasancewa tare da wannan shafin na GORON JUMA’A, shafin da yake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa, har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.

Kamar kowane mako, yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana kamar haka:

  • Mahdi Shehu Ya Buƙaci EFCC Ta Binciki Ɗan Uwan Buhari, Sabiu Tunde
  • Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Zurfafa Kwazo Wajen Aiwatar Da Shirin Raya Kasa Na Shekaru 5 Karo Na 15

Sako daga Isma’il Shitu Jihar Zamfara:

Assalamu Alaikum jaridar Leadership, dan ina so a mika min sakon gaisuwa ta zuwa ga mahaifiyata, da mahaifina, da kuma Yayyena da kannena kamar su; Adda, Atine, Yaya Sambo, Yaya Bello da kuma Ahmadu, da fatan sun yi Juma’a lafiya.

Sako daga Hafsa Kabeer Jihar Kaduna:

Assalam.. Dan Allah a gaishe min da ‘yan’uwa na da abokan arziki irin su; Bilkisu Rabi’u, Zainab Kamal (zeezee), Hussaina, Yaya Dahiru, Kawu Musa ina fatan za su yi Juma’a lafiya, Amin.

Sako daga Rahinatu Junaid Jihar Bauchi:

Ina gaishe da babbar kawata wato Amina Mubarak (Meenah), Nabila Sani, Suhaima, Habiba Kabir, Yaya Faisal, Yaya Ridwan, Yaya Abdulmalik, Aunty Shamsiyya da kuma Suwaiba.

Sako daga Yusuf Garba Jihar Kaduna:

Sakon gaisuwata zuwa ga iyayena sai ‘yan’uwa na kamar su; Yaya Bashi, Yaya Ahmad Yaya Ummi, Yaya Sadiya, Yaya Mubarak, sai kawaye na A’isha, Firdausi, Khadija, Zainab da Yasmin sai malamaina Malam Hassan, Mal. Uzairu, Mal. Lawan, Malama Wasila, Malama Suwaiba, Malama Salma da Malama Ai’sha. Da fatan sun yi juma’a lafiya na gode.

Sako daga Aminu Tijjani Jihar Kano:

Assalamu Alaikum, dan Allah ina son a mika min sakon gaisuwa ta ga abokainai na Yusuf dan badure, Lawan na Eysha, Abdulbasi Munkaila, Sa’ad Idris, Muktar Isah, da kuma Al’amin Sabi’u, da fatan za su yi juma’a lafiya. Sannan ina gaida duk ‘yan gidanmu wato ‘yan’uwana wanda ban fado ba, Allah ya sa mu yi juma’a lafiya.

Sako Daga Aliyu Sadik Jihar Kano:

Ina gaida yayana Yusuf, da umma da Abbana da kuma abomanaina kamar su Muhammad da kuma Usman da Salisu da fatan sun yi juma’a lafiya.

Sako Daga Aisha Sa’eed (Hajiya) Isma’il, Daga Jihar Kaduna:

Ina gaishe da ‘yan’uwana su Fadima da Aliyu, da kanina Abdulsalam da kawayena na makaranta da kuma na unguwarmy da kowa da kowa na fadin duniya al’ummar Musulmi baki daya, da fatan za mu yi juma’a lafiya.

Sako Daga Tijjani Rabi’u Jihar Kano:

Ina gaishe da masoyiyata abar kaunata kuma farin cikin raina Fa’iza Jibril Autar mama, ina gaida abokina Garzali da Abba Ismo da Bilyaminu Lawan, da fatan sun yi juma’a lafiya.

Sako Daga Shukura Aminu Jihar Bauchi:

Ina gaida Habib Isma’il, da Rahma Isma’il, Fauziyya Isma’il, da sauran ‘yan’uwa na makaranta gabadaya. Ina kuma gaida Mamana da Babana Hajiya Hadiza da Alhaji Aminu, ina fatan za su yi juma’a lafiya.

Sako Daga Binta Yusif Jihar Katsina:

Ina gaishe da mutanen kanawa Maryama, Habibah, Saude da Amal. Ina gaishe da kafatanin mutanen Katsina musamman wanda suke ‘yan’uwa na jini da mutanen Jihar Kaduna su ma ‘yan’uwa na jini ina yi musu fatan alkhairi da barka da juma’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *