Harin Sama Na Amurka Mataki Na Farko Ne Na Dakatar Da Ta’addanci A Nijeriya — Moore

[ad_1]

Hare-haren sama da Sojojin Amurka suka kai a Arewa maso Yammacin Nijeriya sun samu martani daga wani ɗan Majalisar Wakilan Amurka, Riley Moore, wanda ya bayyana su a matsayin mataki na farko na kawo ƙarshen kisan jama’a da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.

Moore ya ce hare-haren, da aka aiwatar tare da haɗin gwuiwar Gwamnatin Nijeriya, na da nufin dakatar da ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci, yana mai cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana ƙudurinsa na ganin an kawo ƙarshen kisan Kiristoci a Nijeriya.

  • Rikicin Boko Haram Ya Daɗe Fiye da Yaƙin Basasar Najeriya – Obasanjo
  • Sojoji Sun Ceto ‘Yan Mata 12 Da Boko Haram/ISWAP Suka Sace A Borno

Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya tabbatar da cewa aikin ya gudana ne da goyon bayan Nijeriya, yayin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta ce hare-haren na cikin tsarin haɗin gwuiwar tsaro da ƙasashen waje don yaƙi da ta’addanci.

Moore, wanda ya kai ziyarar bincike a wasu sassan Nijeriya, ya ce rahotannin da ya samu daga al’ummomin da abin ya shafa sun tayar masa da hankali, yana mai cewa zai gabatar da rahoto da shawarwari ga Shugaba Trump kan matakan da ya kamata a ɗauka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *