Nijeriya Ta Tabbatar Da Kai Harin Amurka Kan Ƴan Ta’adda A Sokoto


Gwamnatin Tarayyar ta tabbatar da cewa Amurka ta kai hare-haren sama kan sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar, bayan rahotannin harin bam da aka ce an kai ranar Alhamis. Hakan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya bayar da umarnin kai farmaki kan ƴan ta’addan ISIS da ke kashe Kiristoci a Nijeriya.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar a ranar Juma’a, ta ce hukumomin Nijeriya na ci gaba da haɗin gwuiwa ta tsaro da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, domin fuskantar barazanar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi. Sanarwar ta tabbatar da cewa wannan haɗin gwuiwa ya kai ga kai hare-haren sama na kan wuraren ƴan ta’adda a Arewa maso Yamma.

  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Kada Ta Aiwatar Da Munanan Tanade-tanade Masu Alaka Da Sin A Kudirin Dokar Manufofin Tsaro
  • Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Mai magana da yawun Ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya ce haɗin gwuiwar na gudana ne bisa ƙa’idodin ƙasa da ƙasa da fahimtar juna tsakanin ƙasashe, ciki har da musayar bayanan sirri da tsara dabarun tsaro, tare da girmama ikon ƙasa da dokokin ƙasa da ƙasa. Ya jaddada cewa duk matakan yaƙi da ta’addanci na ƙarƙashin burin kare rayukan fararen hula, da haɗin kan ƙasa, da mutuncin ƴan ƙasa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa duk wani nau’in ta’addanci ko kan Kiristoci ko Musulmi ko sauran al’umma—barazana ce ga ƙimomin Nijeriya da zaman lafiyar duniya.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *