Zulum ya yi Allah wadai da harin ƙunar baƙin wake a masallaci
[ad_1]
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi Allah wadai da harin ƙunar baƙin wake da aka kai a masallacin kasuwar Gomboru da ke birnin Maiduguri a ranar Laraba lokacin magariba.
Wannan hari dai wani ɗan ƙunar baƙin wake ne da ake zargin ɗan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP ne ya kai, ya kutsa kai cikin masallacin ne a yayin da masu ibada ke yin sallar Maghrib, inda ya tada bom ɗin ya kashe mutane biyar tare da raunata wasu 35.
Gwamna Zulum, wanda ke isar da ta’aziyyarsa daga sansanin sojoji a Arewacin Borno ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya ya yi kira da a ƙara taka tsantsan da kuma tsaurara matakan tsaro, musamman a wuraren ibada a lokacin bukukuwan da aka fara.
“Ina matuƙar baƙin ciki da harin ƙunar baƙin wake na masallacin Gamboru wanda ya faru a ranar Laraba da yamma lokacin ga masu ibada ke yin sallar Maghrib, inda ya kashe mutane 5 tare da raunata wasu 35. Wannan aikin abin Allah wadai ne, abin ƙyama ne kuma akwai rashin tausayi tattare da shi,” in ji Zulum.
Ya ƙara da cewa, “Kai hari a wurin ibada ɓata hurumin masallaci ne a lokacin da Musulmai ke yin ibada.”
“Ina so in miƙa saƙon ta’aziyyata ga iyalan duk waɗanda suka rasa rayukansu a harin kuma ina yin addu’ar Allah Ya jiƙansu, da kuma murmurewa cikin sauri ga waɗanda suka ji rauni,” in ji shi.
Gwamnan ya tabbatar da cewa, an ɗauki matakan da suka dace don hana duk wani tashin hankali na tsaro a lokacin bukukuwa da kuma bayan haka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link