Mahdi Shehu Ya Buƙaci EFCC Ta Binciki Ɗan Uwan Buhari, Sabiu Tunde


Masanin harkokin siyasa Mahdi Shehu, ya yi kira ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta binciki Sabiu “Tunde” ɗan uwa kuma tsohon hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kan zargin almundahanar wasu kuɗaɗe.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu, ya ce EFCC ya kamata ta kama Sabiu Tunde ta binciki yadda ya samu dukiyarsa, inda ya ce kafin 2015 ya talaka ne.

  • AFCON 2026: Algeria Ta Lallasa Sudan Da Ci 3 Da Nema
  • CMG Ya Gudanar Da Bikin Gabatar Da Nagartattun Shirye-Shiryensa A Kasashen Ketare

Ya yi gargaɗin cewa ƙimar hukumar na iya raguwa idan ta ci gaba da yin watsi da manyan mutane yayin da take binciko masu ƙananan masu laifi.

Shehu ya ƙara da cewa rashin adalci a fili yana rage amincewar jama’a da yaƙi da cin hanci, kuma yana ƙarfafa wasu su yi amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba.

Kiran nasa na zuwa ne yayin da EFCC ke ci gaba da binciken wasu tsofaffin ministoci da manyan jami’an da suka yi aiki a zamanin shugaba Buhari.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *