An kashe mutum 5 a sabon hari a Binuwai

[ad_1]



Aƙalla mutum biyar aka kashe a wani sabon hari da aka kai wa al’ummar Ortese da ke Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Binuwai.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

Shaidu sun ce wasu ’yan bindiga suka tare hanyar Ortese zuwa Yogbo, sannan suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi a yankin.

Mazauna yankin sun ce maharan sun je da yawa ɗauke da muggan makamai, inda suka kashe samari biyar.

Maharan, sun kuma sace wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba.

Sakamakon harin, mutane da dama sun gudu daga yankin domin tsira da rayukansu.

Wasu mazauna yankin sun ce har yanzu akwai mutanen da ba a san inda suke ba, inda suka buƙaci jami’an tsaro da su yi bincike domin gano waɗanda abin ya shafa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin kama maharan.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici, tare da tabbatar da cewar rundunar ta fara bincike kuma za ta tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata laifin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *