Dole Ne A Hana Yunkurin Japan Na Mallakar Makaman Nukiliya

[ad_1]

A cikin ’yan kwanakin nan, ra’ayoyin kasashen duniya sun yi suka sosai kan kalaman wani babban jami’in kasar Japan na cewa, ya kamata kasar ta mallaki makaman nukiliya. A bisa matakin da gwamnatin Japan mai ci ta dauka mai matukar hadari ga batun mallakar nukiliya, ta kalubalanci tsarin kasashen duniya bayan yakin duniya na biyu da kuma tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na duniya, wanda ya kawo matukar barazana ga zaman lafiya da ci gaban kasa da kasa.

A bangare guda, a matsayinta na kasa mara makaman nukiliya a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, dole ne Japan ta bi ka’idoji na rashin amincewa, da guje wa kerawa, da mallaka, da kuma hana yaduwar makaman nukiliya. A bangare daya kuma, a matsayinta na mai kai hari a yakin duniya na biyu, laifukan tarihi da Japan ta aikata ba a iya kidaya su ba, shi ya sa ba ta da cikakkiyar damar mallakar makaman nukiliya.

Idan Japan ta mallaki makaman nukiliya, hakan zai gurgunta daidaiton tsare-tsaren yankin Asiya da Pasific, da kuma kara haifar da tashin hankali a yankin arewa maso gabashin Asiya da kuma kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin da ma duniya baki daya.

Yunkurin Japan na mallakar makaman nukiliya ba wai kawai ya sake bata wa jama’ar kasashen da yakin ya shafa rai ba ne, har ma zai tayar da zaune tsaye a fili ga zaman lafiya da ci gaban dukkan bil’adama. Idan Japan ta yi abin da duk duniya ke ganin ba daidai ba ne, tabbas kasashen duniya ba za su yarda da hakan ba! (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *