Kotu ta ba da belin wadanda ake zargi da kashe matafiya daurin aure a Mangu




Babbar Kotun jihar Filato mai lamba bakwai ta bayar da belin mutum 20 da ake zargi da kisan matafiya 13 ’yan asalin Zariya a Mangun jihar Filaton lokacin da suke kan hanyar zuwa daurin aure.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Nafisa Lawal Musa, ce ta bayar da belin ranar Alhamis bayan sauraron hujjojin lauyan wadanda ake kara, Garba Pwul (SAN).

An dai yi wa matafiyan kisan gilla ne a ranar 12 ga watan Yunin 2025, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Qua’an Pan domin daurin auren dan uwansu.

Rundunar ’yan sand ace dai ta gurfanar da mutanen a kara mai lamba PLD/115CR/2025, kana laifuka hudu da suka hada da hadin baki, mallakar muggan makamai, da kuma kashe matafiyan su 13.

Masu shigar da kara sun shaida wa kotun cewa laifukan sun saba da tanade-tanaden sassa na 59, da 220, da 313 da kuma 189 na Kundin Dokar jihar Filato na shekara ta 2017.

A baya dai a watan Yuli, lauyan wadanda ake karar, Boniface Ngyong, ya nemi belin mutanen, amma aka hana shi saboda kotun za ta tafi hutu.

Mai Shari’a Nafisa ta ce ta yanke hukuncin bayar da belin nasu ne sakamakon bukatar hakan da wadanda ake kara suka yi, bisa shawarar Daraktan Sashen Gurfanar da Masu Laifi na Ofishin Babban Lauyan Gmamnatin Jihar.

Lauyan wadanda ake karar ya bukaci kotun da ta saki wadanda ake karar ba tare da wani sharadi ba, ko kuma ta sake su har zuwa ranar da kotun za ta dawo zama ranar 13 ga watan Oktoban 2025.

Bayan sauraron lauyoyin, alkalin ta amince da bukatar lauyoyin wadanda ake kara ta biyu, inda ta sake su sannan ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 13 ga watan Oktoba mai zuwa.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *