Mun Kusa Warware Saɓanin Da Ke Tsakaninmu Da Amurka – Gwamnatin Tarayya

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta ce an kusan warware saɓanin diflomasiyya da ya taso tsakaninta da Amurka.

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan a wani taron ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja.

  • An Bullo Da Sabon Daftarin Dokar Kiyaye Muhallin Halittu Na Kasar Sin
  • Kogi Poly Ta Sallami Ma’aikata Biyu Kan Cin Zarafin Jima’i Da Rashin Zuwa Aiki

Ya ce Nijeriya ta tunkari lamarin cikin natsuwa da girmamawa, lamarin da ya ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Idris, ya ce alaƙar ta haifar da sabuwar yarjejeniya ta kiwon lafiya na shekaru biyar tsakanin Nijeriya da Amurka, wadda kuɗinta ya kai dala biliyan 5.1.

A cewarsa, Amurka za ta bayar da tallafin dala biliyan 2.1, yayin da Nijeriya za ta zuba dala biliyan 3 domin inganta harkar kiwon lafiya.

Ya ƙara da cewa wannan ita ce babbar yarjejeniyar haɗin gwiwar kiwon lafiya a ƙarƙashin shirin lafiyar duniya na Amurka, kuma za ta taimaka wajen ceto rayuka, ƙarfafa asibitoci, da zuba jari a Nijeriya.

Ministan ya kuma ce Nijeriya na taka muhimmiyar rawa a fagen duniya, kuma sabbin jakadun da aka naɗa za su fara aiki a ƙasashen da aka tura su a shekarar 2026 domin ƙara ƙarfafa dangantakar diflomasiyya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *