Gwamnan Yobe ya tallafa wa Kiristoci 7,000 da kayan abinci

[ad_1]



Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayan abinci ga Kiristoci 7,000 mazauna jihar domin murnar bikin Kirsimeti.

A cewar shirin rabon tallafin, kowanne daga cikin waɗanda suka ci gajiyar ya samu buhun shinkafa, kwalin taliya, man girki da garin semovita, domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin farin ciki da walwala.

Da yake jawabi a wajen rabon kayan, Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kai Tallafin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dakta Mohammed Goje, ya bayyana cewa Gwamna Buni ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da rungumar zaman lafiya tare da yin addu’a domin ci gaban Jihar Yobe da Najeriya baki ɗaya.

Shi ma mai kula da harkokin ibada na Kiristocin Jihar Yobe, Mista Emmanuel Degubi, ya yaba wa gwamnan bisa wannan taimako, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai kula da al’ummomin Kirista a jihar.

A cewarsa, “A ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Buni, mu al’ummar Kirista mun ci gaba da samun tallafi a lokutan faruwar iftila’i da kuma taimakon shekara-shekara a lokacin bukukuwan Kirsimeti, da sauran nau’o’in tallafi.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *