Kano: Za a hukunta ’yan sandan da aka gani suna karɓar kuɗi a bidiyo




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta ce za ta hukunta wasu jami’anta da aka gani a wani faifan bidiyo suna taimaka wa wani ɗan siyasa wajen shirya jama’a domin karɓar kuɗi.

A wata sanarwa kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ta ce ta binciki lamarin, inda ta gano ya faru ne a wani biki da aka yi a ɗakin taro na Coronation Hall, fadar gwamnatin Jihar Kano, ranar Alhamis 10 ga watan Yuli, 2025.

Rundunar ta ce taron bai da alaƙa da zaɓukan cike gurbi da aka gudanar ranar 16 ga watan Agusta, 2025.

Bincike ya nuna jami’an sun je wajen bikin ne domin tabbatar da tsaro, amma daga baya aka ga bidiyon da ya nuna su suna aikata abin da rundunar ta kira rashin ɗa’a.

Rundunar ta tabbatar da cewa za a ɗauki matakan ladabtar da jami’an domin kare mutunci da martabar rundunar ’yan sandan Najeriya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *