Shekaru 45: Yaƙin Maitatsine ya bar baya da ƙura




“Ya ci zarafinmu sosai. Ɗaya daga cikin abokan zamana Balarabiya ce kyakkyawa, … Sai ya ce zai kusance su, sai su ƙi. A nan zai yi musu dukan tsiya, sannan kuma ya haike musu tsawon kwana bakwan da muka yi a hannunsa.”

Wannan kaɗan ne daga labarin Hajiya Aishatu Adamu (Atine), ɗaya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a gidan Maitatsine a lokacin mummunan rikicin da ya ɓarke shekara 45 da suka gabata a Kano.

haka me

“Muna zaune ya sha zuwa da wuƙa, ya ce wa matansa ‘na yanka wane’. A nan za a wanke masa jinin jikin wuƙar kamar yadda ake wanke allo ya shanye.”

“A nan na samu larurar ido ba na gani sosai, saboda zaman duhu da tashin hankali. Akwai wata ma ta gamu da larurar kunne. Abokiyar zamana shanyewar rabin jiki. Ya ci zarafinmu sosai,” in ji ta.

Hajiya Atine wadda ke da shekaru 22 a lokacin, ta ce Maitatsine ya kama ta da kishiyoyinta ya tsare a gidansa bayan ya kashe mijinsu ta ci gaba da cewa, “Ɗaya daga cikin abokan zamana Balarabiya ce kyakkyawa, … Sai ya ce zai kusance su, sai su ƙi. A nan zai yi musu dukan tsiya, sannan kuma ya haike musu tsawon kwana bakwan da muka yi a hannunsa.”

Rikicin Maitatsine a Kano

Haƙiƙa 18 ga watan Disamba, 1980, rana ce da ta ba za taɓa mantawa da ita ba a tarihin Kano, saboda yaƙin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

A wannan rana ce birnin Kano ya koma filin yaƙi, ba da wata ƙasa daga waje ba, da aƙidar da ta samo asali daga wani da salin ƙasar Kamaru mai suna Muhammad Marwa, wanda aka si sani da Maitatsine.

Rahotanni sun bayyana cewa a kwanaki 11 kacal da aka kwashe ana gabza yaƙin, an kashe kimanin mutane 4,000 ciki har da sojoji da ’yan sanda da fararen hula, baya ga waɗanda aka jikkata da asarar dukiyoyi.

Jaridar New Nigerian, wadda a wancan lokaci ita ta fi tasiri a Arewacin Nijeriya, ta ruwaito cewa a ranar, hukumomin tsaro sun tura rukuni-rukuni na ’yan sanda har huɗu zuwa Filin Shahuci, kusa da Babban Masallacin Juma’a na birnin Kano, inda Maitatsine da mabiyansa ke gudanar da wa’azi ba tare da izini ba, domin kama wasu daga cikinsu.

Da isarsu, almajiran Maitatsine suka yi musu kwanton ɓauna daga kowanne ɓangare, kowannensu ɗauke da aska, kwari da baka, takubba, kulake, wuƙaƙe da sauran makamai masu haɗari.

Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, ta rawaito cewa a daren ranar Alhamis da rikicin ya fara, an kashe jami’ai ’yan sanda huɗu an ƙone motocinsu tara. Harkokin sufuri a Kano a ranar Juma’a da Asabar sun tsaya cak, saboda mutane suna tsoron fita. Ko ma’aikatan lafiya ba su iya zuwa asibiti ba. Kusan ko’ina a birnin Kano da yankin Sabon Gari ya yi tsit.

Rahotannin sun nuna cewa a ranar farko kaɗai, kusan mutane 100 suka mutu, yawancinsu fararen hula, a rikicin wanda daga masallaci, ya kai ga ’yan sanda sun kai hari gidan Maitatsine da ke Ƙaramar Hukumar Birni.

Kwanaki 11 kacal aka kwashe ana gabza yaƙin, wanda rahotanni suka ce an kashe mutane kimain 4,000, ciki har da Maitatsine kansa, da sojoji da ’yan sanda, da kuma mutanen gari.

Yadda Maitatsine ya samu ƙarfi

Malam Maitatsine, wanda ainihin sunansa Muhammadu Marwa, ɗan asalin ƙasar Kamaru ne da ya zauna a Kano ya kuma shahara saboda tsattsauran wa’azinsa na ƙyamar ci-gaban da zamani ya zo da shi da ilimin boko. Yana kuma kiran agogo da rediyo da babur da duk abin da zamani ya kawo a matsayin “Bidi’a” — wato ƙirƙirarren abu a addini.

Da farko ya fara jan hankalin matasa ne musamman almajirai da marasa galihu da salon wa’azinsa na sukar gwamnati da ci gaban zamani. Daga bisani kalamansa sun ɗauki salo na barazana, lamarin da ya sa Sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sanusi I, ya kore shi.

Bayan murabus ɗin Sarki Sanusi a 1963, Maitatsine ya dawo ya zauna a unguwar Ƙoƙi, inda a hankali ya yi ƙarfi.

‘Daga kai ƙarar Maitatsine aka kulle mu’

Kafin ɓarkewar rikicin, al’umar Ƙoƙi sun riƙa lura da abubuwan da yake yi da ba su dace ba, kamar tara mutane da sunan makarantar allo ana cusa musu tsattsauran ra’ayi, da kuma shigowar baƙi ɗauke da makamai.

Dattawan unguwa sun kai ƙara wurare da dama, ciki har da wurin Mataimakin Gwamna na lokacin, Marigayi Bibi Faruk, amma ba a ɗauki mataki ba.

Baba Habibu, wanda ke da shekaru 100 a yanzuu, yana daga cikin dattawan da suka kai wa mataimakim gwamnan ƙorafi, amma a ƙarshe aka tsare su a caji ofis baki ɗayansu.

“Muna ganin ana kawo mutane da daddare wasu kuma da rana. Makamai a hannu. Mun kai ƙara. Mun je wurin gwamnati. An yi burus da mu, har sai da suka yi ƙarfi. Lokacin da na tunkare shi a kan haka, sai ya yi dariya ya ce min: ‘Wa zai hana ni?

“To ana haka wata rana ina kwance, sai ga shi shi da yaransa da ’yan sanda, sai ya ce to ga shi nan taso… aka tafi da ni aka kulle ni.

Mata da yara sun fi shan wuya

Lokacin da rikicin ya tsananta, mata da yara su ne suka fi shan wahala. Hajiya Aishatu Adamu (Atine), wadda ke da shekaru 22 a wancan lokacin, sabuwar uwa ce da jaririyarta ’yar watanni biyu.

Ta ce, “Da farko maɓwabcinmu ne. Mai gidanmu idan ya tashi Zakkah, shi yake fara bai wa. Yana dai kyautata masa sosai. Amma wannan bai hana shi takura mana ba. Wani lokacin sai ya tare hanya. Mu ’yan unguwa suka takura mana. Wani lokacin ma su hana shiga su hana fita. Ko su je masallaci su hana shiga su hana fita. Suka dai takura mana.

“Sai mijinmu ya gaji, saboda idan ka kai shi ƙara kai za a kama. Sai abin ya ishe shi, sai muka tashi daga wannan gidan muka dawo wannan. A nan ƙofar gidanmu suka zo suka tara yashi suka rufe hanya, suka da sa sanda da jan yadi. Ba shiga ba fita.

“To dama mu muna gida a kulle. Kofar gidanmu ne hedikwatarsu. Margayi Nasiru Ahali shi ma ya dawo da mota daga tafiya suka hana shi shiga gidansa. Haka mai gidanmu. To ashe duk mazan an hana su shigowa. Lokacin babu wayar hannu ta landlayin ce.

“Maigidanmu sai ya kasa haƙuri ya ce gaskiya sai ya shigo saboda matansa da ’ya’yansa. Sai ya ajiye motarsa wurin gidan mariya ya taho da kafa. Sai ya zo babu hanya sai ya hauro ta katanga. Daga ranar bai kuma fita ba. Ba mu isa mu yi girki ba ko zubar da ruwa ya bi ta rariya saboda idan muka sake suka san muna nan to kashinmu ya bushe.”

Yadda Maitatsine ya yi wa matan aure fyaɗe — Atine

Bayan an kashe maza da dama, an kwashe mataynsu da ’ya’yansu gidan Maitatsine, inda aka tsare su a cikin duhu, a gidajen mutane da ke kewaye da gidansa da ya ƙwace da ƙarfi.

“Duk gidajen mutane sun gaje. Sai su huda ƙofa su haɗe shi da gidan Maitatsine. Sai aka zo aka tafi da mu. Mun je ba a fi awa huɗu ba sai ga shi da hula da agogon mai gidanmu. Sai ya tambaya ina matansa? Muka ce ga mu. Sai ya ce ya kashe shi. Nan muka fashe da kuka sai ya hau yi mana hargagin faɗa.

“A wani daki a sama mai kamar wurin sayar da itace ya jigbe mu. Babu haske ko kaɗan, amma haka aka danna mu. Ba mu kaɗai ba har da dama daga ’yan unguwar. Ba mu da aikin yi sai girki. Ba mu isa mu yi Sallah ba tunda ba sa yi.

“Haka za su kwaso kayan abincin mutane su kawo mu dafa. Wani lokacin haka za su harbo bindiga harsashi har wajen kafarmu. Ga tiya gas. Haka muka yi baƙiƙƙirin. A nan na samu larurar ido ba na gani sosai, saboda zaman duhu da tashin hankali. Akwai wata ma ta gamu da larurar kunne. Abokiyar zamana shanyewar rabin jiki.

“Ya ci zarafinmu sosai. Ɗaya daga cikin abokan zamana Balarabiya ce kyakkyawa, haka matar Nasir Ahali. Sai ya ce zai kusance su, sai su ƙi. A nan zai yi musu dukan tsiya sannan kuma ya haike musu tsawon kwana bakwan da muka yi a hannunsa.

“Kuma a lokacin ita matar Nasiru Ahalin na shayar da jaririya. Muna zaune ya sha zuwa da wuƙa, ya ce wa matansa ‘na yanka wane’. A nan za a wanke masa jinin jikin wukar kamar yadda ake wanke allo ya shanye. Muna zaune muna kallo.”

Yadda Maitatsine ya titsiye ni a gidansa — Alƙali

Ɗalhatu Muhammad (Alƙali), ɗaya daga cikin dattijan da suka shiga hannun Maitatsine bayan kashe masa ɗansa mai suna Tijjani, wanda ake kira da Kan’ana, ya bada labarin yadda mutuwar Tijjanin ta zama hujjar malamin ta ɗaukar fansa kan mutanen Ƙoƙi.

“Ina wurin sana’ata aka zo aka tafi da ni. Shi kuma ɗayan da ya kashe, dama almajirin gidansa ne. Nan suka kashe shi. Ni kuma sai ya saka ni a gaba yana min tambayoyi. Waye da waye suka kashe masa ɗansa? To dama kullum da ƙarfe huɗu zai fito, akwai wata uwar ɗakinsa ana ce mata Mama. Zai wuce ni ya je ya gaida ta. Yana ganina tare da Tijjanin.

“To da ’yan unguwa suka ga haka, sai da yawa suka tsere. A lokacin ina da shekara 31. Ya dai yi min tambayoyi sosai. Ya ga dai haƙiƙa sana’ata nake yi idan na gama sai na tafi gida.

“Muna cikin haka sai ga wani abokin ɗan nasa ya zo ya yi masa gaisuwa ya fita. To su almajiran sun san shi, shi kuma Maitstinen bai san shi ba. Yana fita ya hau kan mashin dinsa kamar ya san za a kama shi, sai suka faɗa masa, sai ya ce su kamo masa shi ko da ransa ko babu ransa.

“Da yake da kwanansa a gaba, sai Allah Ya taimake shi ya tafi. Da ya dawo kaina sai ya ce min tunda manyan unguwa sun haɗa kuɗi an kashe min ɗana, sai na ɗau fansa a kan kowa. Sai ya zayyano maƙwabtansa baki ɗaya; Margayi Garba Ahali, Margayi Alhaji Yawale, Ɗan Lami Alhassan, Garba Wanzami waɗannan gaba ɗaya sunayensu, ya ce sai ya ɗau fansa a kansu, ko shi kaɗai ne, balle suna da yawa.

“Shi ke nan sai ya sallame ni. Da na taso, mutane duk sun yi tsuru-tsuru (ya tuna yana dariyar takaici) . To tunda na ji abin da ya ce, duk waɗannan da ya zayyano, duk sai da na bi na faɗa musu,” in ji Alƙali

Yadda aka kashe Maitatsine

Bayan ’yan sanda sun kasa shawo kan lamarin, Gwamnatin Jihar Kano ta nemi taimakon Gwamnatin tarayya. Sojoji suka shigo da manyan makamai da jiragen sama masu saukar ungulu.

Hajiya Atine na cikin gidan Maitatsine a wannan lokaci. Ta ce, “Sojoji sun jibge igwa a kusa da gidan, shi kuma ya dinga tura almajiransa sawu-sawu. Haka suka dinga fita ana kashe su har aka rusa katangar gidan.

“Sai ya fara kaɗa mu wai mu yi wani guri, muka ƙi saboda sojojin na ta ce mana mu sunkuya kar harsashi ya same mu. Haka muka dinga gudu cikin gawarwaki.

Haka muka yi wajen Kasuwar Kurmi sojoji suka zube mu a wata rumfa. Wasu ba sa ji wasu ba gani saboda wanan masifar. Daga baya sai Nasiru Ahali ne ya karɓe mu, amma sai da ya yi sintiri har wajen sau uku. Sai gidan Inuwa Dutse aka kai mu.

“A nan muka rasa mai aikina da yarinyarta har yau ban san inda suke ba, amma ina kyautata zaton sun mutu. Kishiyata kuma mai aikinta ta gudu da ’yar don tsira amma daga baya aka samo ta. Amma ni tawa har yau.”

Bayan an raunata Maitatsine, mabiyansa sun ɗauke shi daga Ƙoƙi zuwa Jakara-Goron Dutse, suka nufi unguwar Rijiyar Zaki, inda suka binne shi bayan ya mutu. Daga bisani hukumomi sun tono gawarsa don tabbatar da cewa shi ne da gaske.

Akawai alaƙa tsakanin Maitatsine da ƙungiyoyin ta’addanci — Masani

Masu nazarin harkokin tsaro, sun tabbatar da cewa mutuwar Maitatsine ba ta kawo ƙarshen mummnar aƙidar da ya bari ba, hasalima yaɗuwa ta yi zuwa matakin ƙasa baki ɗaya.

Dokta Yahuza Getso masanin tsaro ne a Najeriya, ya ce tun a shekarar 2002 yake gargaɗin gwamnati kan fantsamar makami ta hanyoyin da ba su dace ba a jihohin Kebbi, Neja, da Zamfara, amma ta yi kunnen uwar shegu.

“Nijeriya ba ta gaza samar da tsaro ba, ta dai ƙi ta yi ne. Hatta matsalar ƙwacen waya da ake yi a wasu jihohin, idan ba a tashi tsaye ba, za su iya zamowa ƙungiyar ta’addanci, su kuma gagara. Don haka rashin aikin yi yana da matuƙar haɗari ga matasa. Don haka ya zama dole gwamnati ta samar da aikin yi.”

Dangane da alaƙa tsakanin ƙungiyoyin ta’addancin da ke fakewa da adini a Nijeriya kuwa, Dakta Getso ya ce abin da ya faru a Kano a 1980 shi ne tushen rikice-rikicen da Nijeriya ke fama da shi a yau.

“Maitatsine ya tafi ne, bai tafi ba. Wato salon nan na ana murna baƙo ya tafi ashe yana bayan gari. Ɗaya daga cikin rauni da kura-kuran da shugabanninmu suke yi a Nijeriya tamkar shukar filawa ce; idan suka tashi kashe ta, sai su bubbuge fulawoyin su karkaɗe ganyen su watsa ma itacen baƙin mai. Sai su ce sun kashe ta bayan sun manta jijiyoyin da saiwar na nan a shuke.

“Don haka idan ka duba ayyukan Boko Haram da ISWAP, har ma da masu sace mutane su karɓi kuɗin fansa, hanyoyi da dabaru ɗaya suke bi da Maitatsine, suna azabtar da mutane, da wulaƙanta ɗan adam, da cin zarafinsa.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *