’Yan sanda sun kama mutum 3 kan zargin satar yara a Borno
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wasu matasa uku da ake zargi da satar yara maza biyu a Ƙaramar Hukumar Jere a jihar.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 16 ga watan Disamba, 2025.
Ya ce an kama matasa ne bayan samun bayanan sirri da kuma zurfafa bincike kan lamarin.
Waɗanda da ake zargin sun haɗa da Abubakar Hassan mai shekaru 19, Modu Aji mai shekaru 18, da Baba Goni Abatcha mai shekaru 18.
An kama su ne a ranar 13 ga watan Disamba, 2025, bisa zargin cewa sun sace yaran a ranar 5 ga watan Disamba, 2025.
Tuni rundunar ta ceto yaran da aka sace.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya yaba wa jami’an rundunar bisa ƙoƙarinsu da jajircewarsu wajen kama masu laifin.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa bayar da sahihan bayanai ga ’yan sanda a kan lokaci domin taimakawa wajen hana aikata laifuka.
Ya tabbatar da cewa suna ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link