Ahmed Musa ya yi ritaya daga buga wa Najeriya ƙwallo
[ad_1]
Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, ya sanar da yin ritaya daga buga wa Najeriya tamaula.
Wannan mataki ya kawo ƙarshen shekara 15 da ya yi yana taka leda tare da Super Eagles.
Ɗan wasan mai shekaru 33, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, bayan wallafa sanarwa a shafukansa na sada zumunta.
Musa, ya ce wakiltar Najeriya a gasa daban-daban abu ne mai matuƙar muhimmanci a tarihin rayuwasa.
Ya tuno yadda ya fara taka leda tun yana matashi, inda ya buga ƙwallo a matakin U-20, U-23 da kuma Super Eagles.
Ya bayyana cewa duk waɗannan matakai da ya bi, bai taɓa ƙorafi ba, duk lokacin da Najeriya ta kira shi yana amsa kiranta da gaggawa.
Ya yi murabus a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa buga wa Najeriya wasanni, inda ya buga wasanni 111.
Musa ya ce wannan babban abin alfahari ne a gare shi.
Musa, ya lashe gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) tare da Najeriya a shekarar 2013, sannan ya kafa tarihi a gasar cin kofin duniya.
Shi ne ɗan Najeriya na farko da ya zura ƙwallaye biyu a wasa guda a gasar cin kofin duniya, bayan zura ƙwallaye biyu a ragar Argentina a 2014.
Daga bisani kuma ya zama ɗan Najeriya na farko da ya ci ƙwallo a gasar cin kofin duniya biyu, bayan ya sake zura ƙwallaye biyu a ragar Iceland a 2018.
Musa, ya gode wa abokan wasansa, masu horaswa, jami’an ƙwallon ƙafa da kuma magoya bayan Najeriya, a gida da ƙasashen waje, bisa goyon bayan da suka ba shi tsawon shekarun da ya yi yana taka leda.
Ya ce ya yi bankwana da buga wa Najeriya tamaula cikin kwanciyar hankali, inda ya yi wa Super Eagles fatan ci gaba da samun nasara.
Musa, ya koma Kano Pillars a watan Oktoban 2024, a karo na uku.
A halin yanzu shi ne babban manajan ƙungiyar, yayin da ake ake ci gaba da buga kakar wasanni 2025/2026.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link