Majalisar Dokokin Akwa Ibom ta yi fatali da ƙudurin neman hana cin naman kare




Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta ƙi amincewa da wani kudiri da ya nemi haramta ci da sayar da naman kare a jihar.

Kudirin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Etinan, Uduak Ekpoufot ya gabatar ranar Talata, bai samu ko da dan majalisa daya da ya mara masa baya ba.

Jaridar nan ta gano cewa Uduak ya roki majalisar da ta yi la’akari da matsalolin kiwon lafiya da ke tattare da cin nama kare, yana gargadin cewa yadda ake yanka dabbobin ba tare da tsafta ba na iya jefa masu cin nama cikin haɗarin kamuwa da cututtuka irin su rabies, salmonella, trichinella da sauran kwayoyin cuta.

Ya kuma bayyana hanyoyin da ake amfani da su wajen kashe karnuka a kasuwancin a matsayin na rashin tausayi.

Duk da hujjojin da ya gabatar, babu wani ɗan majalisa da ya goyi bayan kudirin, lamarin da ya tilasta wa kakakin majalisar ya yi hukunci da cewa an ƙi amincewa da shi.

Akwai dai sassa da dama na Najeriya, musamman a kudancin kasar nan da ma wasu sass ana Arewacin kasar da ke cin nama kare.

A farkon wannan shekara, wani masani kan namun daji, Edem Eniang, ya ce mata ’yan Najeriya suna cin nama kare fiye da maza, bisa wasu al’adu da ke ɗaukar cewa naman yana inganta laushin fata.

Ya ce wannan al’ada ta fara fitowa fili ne a wata lakca da wani masanin dabbobi, Richard King, ya gabatar.

Eniang ya kuma nuna damuwa kan raguwar adadin karnuka saboda yawan cin naman su da ake yi.

Ya ba da misalan wasu lamarin da suka faru a Ibeno da Oron a jihar ta Akwa Ibom, inda aka sace karnuka aka yanka su don abinci, cikin su har da wata karya mai shayarwa da ’ya’yanta ƙanana.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *