Sojoji sun kwace makamai 2,000 a shekara guda

[ad_1]



Sojoji sun kwace bindigogi da sauran makamai sama da 2,000 a cikin shekara guda da ta gabata a jihohin Kaduna da Bauchi da Filato.

Rundunar tsaro ta Operation SAFE HAVEN (OPSH), wadda ke tabbatar da zaman lafiya a ta bayyana cewa ta kama jimillar makamai 220, alburusai 1,874 da kwanson harsasai 83 daga watan Janairu 2024 zuwa yanzu.

Kwamandan OPSH kuma Babban Hafsan Rundunar Sojin Najeriya na Division ta 3, Manjo Janar Folusho Oyinlola, ne ya bayyana hakan yayin da yake mika makaman ga Hukumar Kula da Yaduwar Makamai da Karamin Bindiga (NCCSALW) a hedikwatar OPSH da ke Jos.

Manjo Janar Oyinlola ya ce wannan mataki na daga cikin kudurin Gwamnatin Tarayya na dakile zubar da jini da rashin tsaro da ke faruwa sakamakon yaduwar makamai a cikin al’umma.

Ya kara da cewa rundunar ta samu gagarumar nasara wajen dakile hare-haren ’yan ta’adda ta hanyar amfani da dabarun tsaro na soji da kuma na diflomasiyya.

“An kwato makamai 220 daga hannun masu laifi tun daga farkon shekarar 2024 zuwa yanzu. Haka kuma an kama alburusai 1,874 da harsasai 83,” in ji shi, yana mai kira ga al’umma da su goyi bayan kokarin kawar da makamai ba bisa ka’ida ba domin samar da al’umma mai zaman lafiya.

A nasa jawabin, Mataimakin Darakta Janar na NCCSALW, Mr Abdul Adamu, wanda ya wakilci Darakta Janar, ya yaba da kokarin OPSH wajen yaki da masu dauke da makamai ba bisa ka’ida ba da kuma dakile yaduwar su a yankin da rundunar ke aiki.

Ya kuma bukaci al’umma da su mara wa Gwamnatin Tarayya baya wajen kawar da makamai ba bisa ka’ida ba daga cikin al’umma baki daya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *